Duniya
1 minti karatu
Trump na shan caccaka bayan ya ‘zagi’ Lesotho
Lesotho ta yi Allah wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump inda ya ce an bayar da tallafin dala miliyan takwas ga ƙasar da “babu wanda ya taɓa jin labarinta”.
Trump na shan caccaka bayan ya ‘zagi’ Lesotho
Lesotho ƙasa ce a Afirka wadda ke da kyawawan tsaunuka tana kuma da kusan mutum miliyan biyu.
3 часа назад

Lesotho ta yi Allah wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump bayan ya ce kasa ce a Afirka da ''ba wanda ya taba jin labarinta''. Ƙasar ta ce wannan cin mutunci ne.

Trump ya ambaci Lesotho a cikin jawabin da ya yi wa Majalisar Dokokin Amurka a yammacin Talata yayin da ya lissafa wasu kuɗaɗen da ake kashewa ƙasashen ƙetare da ya rage, abin da ya kira da “mummunan almubazaranci”.

Ya yi magana kan wani tallafi ɗaya da aka bayar na dala miliyan takwas “a ƙasar Afirka Lesotho, da ba wanda ya taɓa jin labarinta.” Wannan ya jawo ‘yan majalisa sun rinƙa dariya game da lamarin.

Ministan Harkokin Wajen Lesotho Lejone Mpotjoane ya ce ya girgiza bayan ya ji abin da Trump ya ce, inda ya gayyaci shugaban na Amurka ya kai ziyara ƙasar. Mpotjoane ya ce maganar ta Trump “kamar zagi” ce.

“Na yi matuƙar kaɗuwa da cewa shugaban ƙasa na iya kiran kasarta haka," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Lesotho ƙasa ce a Afirka wadda ke da kyawawan tsaunuka tana kuma da kusan mutum miliyan biyu.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us