Nijeriya
2 minti karatu
Kwamitin Majalisar Dattawan Nijeriya ya yi watsi da ƙorafin Sanata Natasha kan Akpabio
Kwamitin a ranar Laraba ya bayar da hujjojin da ya sa ya yi watsi da ƙorafin waɗanda suka haɗa da saɓa ka’idojin da ya kamata ta bi wurin gabatar da ƙorafin da matakai na shari’a.
Kwamitin Majalisar Dattawan Nijeriya ya yi watsi da ƙorafin Sanata Natasha kan Akpabio
Kwamitin ya ce ƙorafin da Natasha ta gabatar yana a gaban kotu wanda hakan wani ƙarin dalili ne da zai sa a yi fatali da ƙorafin a majalisar.
7 saat əvvəl

Kwamitin Majalisar Dattawan Nijeriya kan ɗa’ar ‘yan majalisa da karɓar ƙorafe-ƙorafe ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar game da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, inda kwamitin ya ce “ba shi da amfani”.

Kwamitin a ranar Laraba ya bayar da hujjojin da ya sa ya yi watsi da ƙorafin waɗanda suka haɗa da saɓa ka’idojin da ya kamata ta bi wurin gabatar da ƙorafin da matakai na shari’a.

Shugaban kwamitin da ya yi bincike kan lamarin, Sanata Neda Imasuen, ya ce doka mai lamba 40 ta Majalisar Dattawa da Sanata Natasha ta yi amfani da ita wurin gabatar da ƙorafin, da kanta ta saka hannu kan takardar ƙorafin maimakon ta bai wa wani ɗan majalisa ya saka hannu a kai ya goyi bayanta, wanda hakan ya sa ba za a karɓi ƙorafin ba.

Haka kuma ya ce ƙorafin da Natasha ta gabatar yana a gaban kotu wanda hakan wani ƙarin dalili ne da zai sa a yi fatali da ƙorafin a majalisar.

A ranar Laraba ne Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Godswill Akpabio ya musanta zargin cin zarafi ta hanyar lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi a kansa.

Ya musanta zargin ne a ranar Laraba bayan majalisar ta koma aiki daga gajeren hutun da ta tafi.

Sanata Akpabio ya nuna rashin jin daɗinsa game da abubuwan da ke yawo a shafukan sada zumunta kan zargin da ake masa inda ya yi watsi da shi baki ɗaya.

“Ban taɓa cin zarafin wata mace ba. Na samu tarbiyya daga mahaifiyata, kuma ina girmama mata. An taɓa ba ni lambar yabo ta gwamnan da ya fi kyautata wa mata a Nijeriya,” kamar yadda Sanata Akpabio ya bayyana.

Bayan nan ne sai Sanata Natasha ta miƙe tsaye ta gabatar da korafi a kansa a hukumance a gaban majalisar bisa zarge-zargen da take masa.

A yayin da take gabatar da ƙorafin, ta zargi Akpabio da cin zarafi ta hanyar lalata da amfani da ƙarfin iko ba bisa ƙa’ida ba da kuma tauye mata haƙƙinta na gudanar da ayyukan majalisa.

Bayan ta gabatar da ƙorafin sai shugaban majalisar ya buƙaci kwamitin majalisar kan kula da ɗa’ar ‘yan majalisa da karɓar ƙorafe-ƙorafe ta yi aiki kan zargin.

Wannan na zuwa ne bayan an shafe kwanaki ana ce-ce-ku-ce kan wannan lamarin bayan Sanata Natasha ta yi wannan zargin a wani gidan talabijin a Nijeriya.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us