Gabas Ta Tsakiya
2 minti karatu
Isra'ila ta rusa gidajen Falasɗinawa a ranar farko ta azumin Ramadan
Nihad Al-Shawish, shugaban wani kwamiti a sansanin Nour Shams ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa “motocin buldoza da dama na sojoji sun afka unguwar al-Manshiya, inda suka lalata hanyoyi da rusa wasu gidaje.”
Isra'ila ta rusa gidajen Falasɗinawa a ranar farko ta azumin Ramadan
Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Falasɗinu a kullum waɗanda akasarinsu mata ne da yara
2 март 2025

A ranar farko ta watan Ramadan, motocin buldoza sun shiga sansanin 'yan gudun hijira na Nour Shams da ke Yammacin Kogin Jordan, inda suka rusa gidaje tare da farfasa hanyoyi a unguwar al-Manshiya.

Nihad Al-Shawish, shugaban wani kwamiti a sansanin Nour Shams ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa “motocin buldoza da dama na sojoji sun afka unguwar al-Manshiya, inda suka lalata hanyoyi da rusa wasu gidaje.”

Ya ƙara da cewa sojojin na Isra’ila sun tilasta wa mazauna sansanin na Nour Shams domin barin wurin, inda suka ce suna shirin “tayar da bama-bamai masu yawa.”

 “Sojoji sun umarci dukkan mazauna sansanin da su fice,” in ji Shawish.

Hare-haren da sojoji ke kai wa Nour Shams yanzu ya shiga kwana na 21, yayin da sojojin Isra'ila suka shafe fiye da wata guda suna kai hare-hare a garuruwan arewacin Yammacin Kogin Jordan, musamman Jenin da Tulkarem, a ci gaba da farmakin da sojoji ke ci gaba da kaiwa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 64 tare da raba dubbai.

A ranar 23 ga Fabrairu, tankokin yaƙin Isra'ila sun shiga sansanin 'yan gudun hijira na Jenin inda rabon da a ga irin wannan tun 2002.

Hukumomin Falasɗinu sun yi gargaɗin cewa ci gaba da kai hare-haren da Isra’ila ke yi na daga cikin shirin gwamnatin Netanyahu na faɗaɗa iyakokin Isra’ila da kuma mamaye Yammacin Kogin Jordan.

Wannan harin dai shi ne na baya bayan nan a hare-haren da sojoji suka kai a Yammacin Kogin Jordan, inda aƙalla Falasdinawa 927 suka mutu, yayin da kusan 7,000 tun bayan fara kai hare-hare kan zirin Gaza a ranar 7 ga Oktoban 2023 a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us