Gabas Ta Tsakiya
2 minti karatu
Isra'ila za ta dakatar da shigar da dukkan kayayyakin agaji yankin Gaza
Ofishin Firaministan Isra'ila bai yi ƙarin haske kan matakin ba, sai dai ya yi gargaɗin “ƙarin abin da zai biyo baya" idan kungiyar Hamas, ba ta amince da abin da Isra'ila ta kira da shawarar Amurka na tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta ba.
Isra'ila za ta dakatar da shigar da dukkan kayayyakin agaji yankin Gaza
Har yanzu ɓangarorin biyu ba su cim ma matsaya kan ko za su shiga zagaye na biyu na tattaunawar tsagaita wuta ba
2 mars 2025

Isra’ila a ranar Lahadi ta ce za ta dakatar da shigar duk wasu kayayyakin agaji da sauran kayayyaki cikin Gaza.

Ofishin Firaministan Isra'ila bai yi ƙarin haske kan matakin ba, sai dai ya yi gargaɗin “ƙarin abin da zai biyo baya" idan kungiyar Hamas ba ta amince da abin da Isra'ila ta kira da shawarar Amurka kan tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta ba.

Sai dai babu tabbaci kan ko zuwa yanzu an dakatar da kai agajin baki ɗaya.

Har yanzu ɓangarorin biyu ba su cim ma matsaya kan ko za su shiga zagaye na biyu na tattaunawar ba, inda a nan ne ake sa ran Hamas za ta saki sauran fursunonin da take riƙe da su sai kuma Isra’ila ta janye baki ɗaya domin samun yarjejeniyar tsagaita wuta mai ɗorewa.

Tattaunawar da ba a kammala ba

Isra'ila ta amince da wani kudiri a ranar Lahadi na tsawaita tsagaita bude wuta a Gaza na wani dan lokaci a matsayin wani mataki na daidaitawa bayan matakin farko na tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ya kawo karshe.

A karshen mako ne dai kashi na farko na shirin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas zai kare ba tare da tabbas kan kashi na biyu ba, wanda ake fatan kawo karshen yakin na dindindin.

Ya zuwa yanzu dai tattaunawar ba ba a kammala ta ba, inda har yanzu babu tabbaci game da makomar mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma rayukan Falasdinawa fiye da miliyan biyu.

Ita kuwa Hamas ta dage kan aiwatar da matakin tsagaita wuta na biyu.

 

 

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us