Nijeriya
2 minti karatu
An fara bincike kan wani mutum da ake zargin ya kashe matarsa kan abincin buɗa-baki a Bauchi
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce ta kama wani mutum mai shekara 50 kan zarginsa da kashe matarsa ta biyu 'yar shekara 24 ta hanyar buga mata sanda a lokacin da suke gardama kan kayan da za a yi amfani da su na abincin buɗa-baki.
An fara bincike kan wani mutum da ake zargin ya kashe matarsa kan abincin buɗa-baki a Bauchi
‘Yan sandan sun ce tuni aka kama mutumin da ake zargi tare da gano sandar da ake zargin ya yi amfani da ita.
2. mart 2025

 Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Bauchi ta ƙaddamar da bincike kan zargin da ake yi wa wani mutum na kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Bauchi CSP Ahmed Wakil ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar 1 ga watan Maris a Fadamam Mada a kusa da makarantar ‘yan mata ta GGC Bauchi.

“Rahotanni sun ce wanda ake zargi Alhaji Nuru Isah, wanda ɗan kasuwa ne a Babbar Kasuwar Bauchi, ya doki matarsa ta biyu mai suna Wasila Abdullahi bayan sun yi sa-in-sa a tsakaninsu kan kayan da za a yi amfani da su na abinci domin buɗa-baki.

 “Daga nan ne rikicin ya yi ƙamari inda ake zargin Isah ya ɗauki sanda ya buga wa matar, lamarin da ya sa ta faɗi ta suma a cikin gidan,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

CSP Wakili ya ce nan take aka garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jam’iar Tafawa Balewa inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarta.

 ‘Yan sandan sun ce tuni aka kama mutumin da ake zargi tare da gano sandar da ake zargin ya yi amfani da ita.

Haka kuma an kai gawar matar ɗakin ajiyar gawawwaki kafin a gudanar da bincike a kan gawar, kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us