Gabas Ta Tsakiya
5 minti karatu
Me shirin Masar kan Gaza ya ƙunsa?
An tattauna shirin a wani taron Larabawa ranar Talata, kuma daga baya shugabannin  sun amince da shi, domin maye gurbin shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya fitar a watan da ya gabata na karɓe iko da zirin Gaza da yaƙi ya ɗaiɗaita kuma ya raba
Me shirin Masar kan Gaza ya ƙunsa?
Shirin ya fitar da matakai biyu: mataki na farko na farfaɗowa da kuma mataki na biyu na sake gini.
March 5, 2025

Masar ta fitar wani shiri na dala biliyan 53 na sake gina Gaza cikin fiye da shekara biyar, inda shirin zai mayar da hankali kan taimakon gaggawa, dawo da ababen more rayuwa da kuma ci-gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa, kamar yadda wani daftari na aiki ya nuna.

An tattauna shirin a wani taron Larabawa ranar Talata, kuma daga baya shugabannin  sun amince da shi, domin maye gurbin shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya fitar a watan da ya gabata na karɓe iko da zirin Gaza da yaƙi ya ɗaiɗaita kuma ya raba mutanenta da muhallanesu, har zuwa Masar da Jordan.

Falasɗinawa, da ƙasashen Larabawa da kuma gwamnatoci da yawa a duniya, sun yi Allah wadai da shirin Trump, inda suka yi watsi da duk wani shiri na korar mutanen Gazan.

Matakin farko na farfaɗowa

Shirin, wanda majiyoyin diflomasiyya suka yayata, ya fitar da matakai biyu: matakin farfaɗowa da wuri da kuma mataki na sake gine.

Mataki na farfaɗowa da wuri, wanda ake sa ran zai kai wata shida kuma zai ci kuɗin da ya kai dala biliyan 3, zai mayar da hankali kan "cire nakiya da aka binne da kuma bama-bamai da ba su tashi ba da share tarkace da kuma samar da gidaje na wucin gadi ".

Domin biyan buƙatun muhalli nan take a wannan matakin, Masar tana ba da shawarar kafa sansanoni bakwai cikin Gaza domin samar wa mutum sama da miliyan 1.5 da gidajen wucin gadi, inda ko wanne gida zai iya ɗaukar mutum shida.

Shirin kuma ya ƙunshi fara gyra gidaje 60,000 da ɓangarorinsu suka lalace domin samar wa mutum 360,000 muhalli.

Matakin sake gini

Matakin sake gini za a yi shi ne a zango biyu cikin shekaru huɗu da rabi.

Zango na ɗaya, da zai kai shekarar 2027 da kasasfin kuɗi da ya kai dala biliyan 20, zai mayar da hankali ne kan sake gina muhimman ababen more rayuwa ciki har da hanyoyi. Shirin kuma ya kuma nemi a gina rukunin gidaje na din-din-din 200,000 wa mutane 1.6 million tare da samu fili da ya kai kadada 20,000 ta hanyar cike teku.

Zango na biyun kuwa, wanda zai kai shekarar 2030 kan kuɗi da ya kai kimanin dala biliyan 30, domin ƙarasa ayyukan samar da ababen more rayuwada gina wasu rukunnin gidaje 200,000 tare da samar da wani yanki na masana’antu da tashan jirgin ruwa na kama kifaye da tashan jirgin ruwa na kasuwanci da kuma filin sauƙa da tashin jirage.

Kuɗaɗe

Shirin ya ba da shawarar samar da asusun da ƙasashen duniya za su sa wa ido domin tabbatar da ingantaccen hanya mai ɗorewa na samar wa shirin kuɗi, tare bin gaskiya da kuma sa-ido.

 

Kazalika birnin Alƙahira za ta karɓi baƙuncin wani taron ministoci domin haɗa kan ƙasashe masu ba da tallafi da cibiyoyin kuɗi na ƙasa-da-ƙasa da kuma na yanki da kamfanoni da ‘yan kasuwa da kuma ƙungiyoyin fararen hula domin tabbatar da samun kuɗi.

Kafar watsa labarn Al-Qahera News mai alaƙa da gwamantin ƙasar Masar ta ba da rahoton cewa sanarwar bayan taron da aka fitar bayan taron Larabawan ya yi maraba da yin taron a birnin Alƙahira nan gaba cikin wannan watan.

Wa zai jagoranci Gaza?

A ƙarƙashin shirin Masar, za a ture ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa, Hamas, gefe kuma za maye gurbinta da wani kwamiti ma’aikata masu cin gashin kansu da kuma waɗanda ba su da alaƙa da siyasa. Kwamitin, kamar yadda daftarin ya tsara, za a kafa shi ne a ƙarƙashin hukumar Falasɗinawa domin jagorantar garin na wata shida.

Sannan hukumar Falasɗinawa za ta fara jan ragamar zirin Gazan. Hukumar Falasɗinawa ta mulki Gaza kafin Hamas ta fara mulkinta a shekarar 2007.

Kamar yadda daftarin ya tsara, Masar da Jordan suna bai wa dakarun da ke da alaƙa da hukumar Falasɗinawa horo domin su fara tabbatar da tsaro a Gaza. Shirin ya kuma yi kira da a ba da tallafi daga ƙasashen waje da kuma yankin domin samar wa shirin kuɗi.

Shirin kuma ya nuna yiwuwar samun ‘yan ƙasashen waje a Falasɗinu, ciki har da yiwuwar samun wani ƙudirin kwamitin tsaro na MDD na tura dakarun kiyaye zaman lafiya Gaza da kuma gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Wannan zai kasance wani ɓangare na wani shiri mai faɗi "da zai kai ga samar da ƙasar Falasɗinawa na din-din-din  da kuma gina ƙarfin ikonta ".

Shirin ya amince da kasancewar ƙalubalen da ɓangarori masu makamai ke janyowa a Gaza, yana mai cewa za a iya magance matsalar ta hanyar "yarjejeniyar siyasa mai mai tushe " wadda za ta mayar wa Falasɗinawa haƙƙinsu tare da samar da hanyar ci-gaba.

Daftarin sanarwar bayan taro na taron Larabawan ya kuma yi kira ga yin zaɓe a Falasɗinu cikin shekara idan har an sami yanayin da ya dace, in ji kafar mai alaƙ gwamnatin ƙasar.

Ranar Talata, Shugabn Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya ce za a yi zaɓen shugabn ƙasa da na ‘yan majalisu wa hukumar Falasɗinawa a shekara mai zuwa, kimanin shekaru ashirin bayan an yi zaɓe a Falasɗinu.

 

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us