Kashi uku cikin hudu na dukkan matasan da ke fama da mummunar ƙiba za su kasance a yankuna biyu — Arewacin Afirka, Gabas ta Tsakiya. Latin Amurka da kuma Karibiyan — nan da shkearar 2050,kamar yadda wani bincike da aka wallafa a mujallar lafiya ta Lancet ya yi gargaɗi.
Binciken ya yi amfani da bayanan da aka tattara daga ƙasashe 204 don fayyace abin da ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen lafiya na wannan ƙarnin.
Dama tuni rabin manya masu fama da mummunar ƙiba a duniya suna zaune ne a ƙasashe takwas da suka haɗa da Masar da China da Indiya da Amurka da Brazil da Rasha da Mexico da kuma Indonesiya, in ji binciken.
Jagorar mawallafan binciken Emmanuela Gakidou, daga Cibiyar Lafiya ta Institute for Health Metrics and Evaluation (IHME) ta Amurka, a wata sanarwa ta ce “Annobar mummunar ƙiba da teɓa da ba a taɓa ganin irinta ba a duniya babban bala’i ne kuma yana nuna gazawar al’umma.”
Yawan masu mummunar ƙiba da teɓa a faɗin duniya ya ƙaru daga miliyan 929 a shekarar 1990 zuwa biliyan 2.6 a 2021, kamar yadda binciken ya gano.
Tasirin hakan ga duniya
Idan har ba a samu wani babban sauyi ba, masu binciken sun ƙiyasta cewa mutum biliyan 3.8 ne za su kamu da mummuar ƙiba da teɓa nan da shekara 15 — ko kuma kashi 60 cikin 100 na yawan al’ummar manya na duniya.
Sannan masu binciken sun yi gargaɗin cewa tsare-tsaren lafiya na duniya za su durƙushe saboda cunkoso, kazalika ana hasashen kusan kashi uku cikin huɗu na masu teɓe a duniya za su kasance ‘yan fiye da shekara 65 ne a lokacin.
Sun kuma yi hasashen ƙaruwar ƙiba da teɓa da kashi 121 a tsakanin yara da matasa a duniya.
Amma ba a makara ba wajen ɗaukar mataki, in ji ɗaya daga cikin marubutan binciken Jessica Kerr daga Cibiyar Nazarin Yara ta Murdoch a Australia.
Mayar da hankali a gwamnatance
"Ana buƙatar dagewa da mayar da hankali a gwamnatance don canza tsarin abinci a cikin tsarin abinci mai ɗorewa na duniya," in ji ta.
Hakanan ana buƙatar wannan sadaukarwar don dabarun "da ke inganta tsarin abincin mutane da motsa jiki, da muhallin rayuwa, ko abinci ne da aka sarrafa da yawa ko kuma rashin isassun wuraren shakatawa," in ji Kerr.
Duk da yake tsarin cin abinci barkatai da rashin tsarin rayuwa mai kyau su ke haifar da annobar ƙiba, "akwai shakku" game da musabbabin hakan, in ji Thorkild Sorensen, wani mai bincike a Jami'ar Copenhagen da bai shiga cikin sabon binciken ba.
Binciken ya samo asali ne daga alkaluman bincike na Global Burden of Disease na IHME, wanda ya hada dubban masu bincike a fadin duniya kuma Gidauniyar Bill da Melinda Gates ce ke daukar nauyinsa.