Nijeriya
2 minti karatu
An kama wasu ‘yan Pakistan biyu kan zarginsu da jagorantar gungun masu garkuwa da mutane a Legas
Kwamishinan ‘yan sanda Olohundare Jimoh ya yaba da matakin da jami’an sashin na Ikeja suka dauka wajen kama mutanen tare da tarwatsa ayyukan ‘yan kungiyar.
An kama wasu ‘yan Pakistan biyu kan zarginsu da jagorantar gungun masu garkuwa da mutane a Legas
Olohundare Jimoh
3 گھنٹے قبل

A wani gagarumin ci gaba na yaki da miyagun laifuka, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta Nijeriya ta ce ta kama wasu ‘yan kasar Pakistan biyu da ake zargi da jagorantar wata muguwar kungiyar masu garkuwa da mutane da ke aiki a birnin.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar CSP Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Alhamis, ta ce kamen ya yi daidai da umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasar, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, wanda ya yi kira da a dauki ƙwaƙƙwaran mataki na murkushe masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a fadin Nijeriya.

Kwamishinan ‘yan sanda Olohundare Jimoh ya yaba da matakin da jami’an sashin na Ikeja suka dauka wajen kama mutanen tare da tarwatsa ayyukan ‘yan kungiyar.

“Wannan aikin da aka samu nasara ya nuna jajircewarmu na tabbatar da tsaro da aminci ga mazauna Legas da masu ziyara,” in ji shi.

"Za mu ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da cewa duk mutanen da ke yankinmu sun sami kwanciyar hankali."

Kamen na baya bayan nan ya zo ne a matsayin martani ga karuwar damuwar da ake samu game da matsalar sace-sacen jama’a a yankin, lamarin da ya kara jaddada aniyar ‘yan sanda na magancewa da kuma kawar da wannan barazana.

CP Jimoh ya nanata cewa rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta dukufa wajen tabbatar da doka da kuma tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

CSP Benjamin Hundeyin, a sanarwar ya nuna jin dadinsa ga al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka bayar da hadin kai yayin gudanar da bincike.

Ya kara da cewa, “Hadin gwiwar jama’a da jami’an tsaro na da matukar muhimmanci wajen yakar miyagun laifuka yadda ya kamata,” in ji shi.

Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, hukumomi sun bukaci duk wanda ke da wani bayani da ya shafi garkuwa da mutane ko wasu abubuwan da ake zarginsa da su da su kai rahoto ga ‘yan sanda cikin gaggawa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta dukufa wajen tabbatar da adalci da kuma tabbatar da an gurfanar da wadanda ke barazana ga al’umma ta hanyar aikata miyagun laifuka,a gaban ƙuliya.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us