Kasuwanci
1 minti karatu
Man fetur ɗin da Nijeriya ke samarwa OPEC ya karu da ganga 70,000 a watan Fabrairu- Reuters
Duk da kalubalen da Nijeriya ke fuskanta ta fuskar yawan sata da fasa bututun mai, yawan albarkatun man da take fitarwa ya nuna yadda karfinta yake a kasuwar mai ta duniya.
Man fetur ɗin da Nijeriya ke samarwa OPEC ya karu da ganga 70,000 a watan Fabrairu- Reuters
ARCHIV: Wani Tsara da ke Nuna Wani Barrel Nùn da Àlàmù Kungiyar Kasashen Mabuɗin Kùyanga (OPEC) a Lokacin Taron Yanayin Hawa Ruwa COP29 na Majalisar Dinkin Duniya a Baku, Aserbijan
5 小时前

Binciken da aka fitar a ranar Laraba, ya sanya Nijeriya a matsayin kasa ta biyu a jerin kasashe mambobin OPEC da ke fitar da albarkatun mai.

Jimillar man fetur da OPEC ta fitar ya kai ganga miliyan 26.74 a watan Fabrairu, adadin da ya karu da ganga 70,000 da Nijeriya ta fitar a watan Janairu. Iran ce kan gaba da ƙarin ganga 80,000.

Rahoton ya danganta yawan man da Nijeriya ke samarwa bisa ga danyen man da take fitarwa zuwa kasashen ketare da kuma yawan amfanin man a cikin gida, musamman matatar man Dangote da ke samar da ganga 650,000 a kullum.

Kungiyar OPEC -  wadda ta haɗa kasashen Larabawa masu arzikin man fetur da Rasha, da sauran abokan haɗin gwiwarta – tana ci gaba da takaita man da ake fitarwa saboda damuwa kan karancin bukatarsa da yadda kasashen da ba sa kungiyar suke kara abin da suke fitarwa. Ko da yake OPEC na shirin kara yawan adadin man da take fitarwa a watan Afrilu.  

Duk da kalubalen da Nijeriya ke fuskanta ta fuskar yawan sata da fasa bututun mai, yawan albarkatun man da take fitarwa ya nuna yadda take dada samun karfi a kasuwar mai ta duniya.

 

TUSHEN:REUTERS
Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us