Jami'an kiwon lafiya sun ce Falasdinawa biyu ne suka mutu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon luguden wuta da sojojin Isra'ila suka yi a kudancin Zirin Gaza a ranar Litinin, a ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma musayar fursunoni.
Wata majiyar kiwon lafiya ta ce mutum biyu sun rasa rayukansu a wani harin da jirgin yaki maras matuki ya kai a tsakiyar birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Wasu ƙarin mutum uku sun jikkata a wani harin makami mai linzami a yammacin Khan Younis da ke kudancin Gaza, in ji likitoci.
Sojojin Isra'ila sun zafafa kai hare-hare a fadin Gaza tun ranar Lahadi, jim kadan bayan karewar kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Ko a ranar Lahadi ma, Falasdinawa hudu aka kashe a irin wadannan hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza.
Gwamnatin Isra'ila ta dakatar da shigar da kayan agaji a Gaza a ranar Lahadin da ta gabata yayin da firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ƙi fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta.
Yarjejeniyar ta dakatar da yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ya kashe mutane fiye da 48,380, galibi mata da kananan yara, tare da mayar da yankin kufai.
A watan Nuwamban da ya gabata ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kama Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant bisa laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Har ila yau Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan kiyashi a kotun kasa da kasa kan yakin da ta ke yi da yankin.