Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ƙaryata wani labari da ke yawo a manhajar WhatsApp da sauran kafafen sada zumunta da ke iƙirarin cewa akwai ‘yan ta’adda 79 a unguwar Lugbe da ke Birnin Tarayyar ƙasar, Abuja.
Wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ranar Lahadi da maraice ta ce “wannan labarin gaba ɗayansa ba gaskiya ba ne kuma ya kamata a yi watsi da shi.”
Sanarwar ta ce bayanan sirrin da jam’ian ‘yan sanda suka tattaro sun nuna cewa babu ‘yan ta’adda da ke samun mafaka a unguwar Lugbe da ke Birnin Tarrayyar Nijeriya, Abuja.
Ta ƙara da cewa saƙon da ke iƙirarin cewa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanya wa sanarwar hannu ba gaskiya ba ne.
“Rundunar ‘yan sandan ta yi imanin cewa wasu mayaudara ne suka ƙirƙiro wannan labari domin tayar da hankulan jama’a da kassara kwanciyar hankalin da ake yi a Birnin Tarayya,” in ji sanarwar.
“Muna kira ga ‘yan ƙasa su yarda da labarai da kuma bayanai daga shafukan da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ke amfani da su a shafukan sada zumunta waɗanda suka haɗa da @PoliceNG a shafin X da @ngpolice a shafin Facebook da kuma @nigeriapoliceforce a shafin Instagram tare da tabbatattun kafafan watsa labarai,” in ji Adejobi.
Ya ƙara da cewa rundunar ‘yan sandan ta duƙufa wajen tabbatar da tsaron dukkan mazauna Birnin Tarayya da ma ƙasar gaba ɗaya.
“Muna ƙarfafa wa mutane gwiwa su mayar da hankali kuma su ba da rahoton duk wani abin tuhuman da suka gani a ofishin ‘yan sanda da ya fi kusa da su ko kuma ta lambobin ko-ta-kwana,” in ji sanarwar.