27 Agusta 2025
Yayin da yake zanta wa da TRT Afrika Hausa, gwamnan wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Jam’iyyar ta PDP, ya faɗi ra'ayinsa kan neman tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takara a 2027, yana mai cewa suna "shiri mai ƙarfi" domin kayar da Shugaba Bola Tinubu na Jam’iyar APC mai mulki a babban zaɓen da ke tafe.