26 Yuni 2025
Idan za a tuna a ranar Litinin da ta gabata ne Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami guda shida a sansanonin sojin Amurka da ke Qatar, domin yin ramuwar gayya kan harin da Amurkar ta kai wa cibiyoyin makaman nukiliyar Iran a karshen makon jiya.
Shin, kun san cewa Amurka tana da cibiyoyi da sansanonin soji birjik a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Mun zayyano muku su daki-daki.