Yadda Ethiopia ta cika burinta na samar da isasshiyar alkama
Kasuwanci
5 minti karatu
Yadda Ethiopia ta cika burinta na samar da isasshiyar alkamaEthiopia ta bunkasa samar da alkama a cikin gida a karkashin Shirin Cigaban Samar da Alkama, inda ta kawar da bukatar shigo da ita kasar daga kasashen waje ta hanyar kara yawan gonaki da iri mai jure zafin rana, inda take yaki da matsalolin jin kai.
Ethiopia is on course to save nearly US $1 billion it used to spend annually on wheat imports as domestic production increases.
3 مارچ 2025

Daga Coletta Wanjohi

Ko kana rayuwa a birnin mai cunkoso ko a kauyen Ethiopia, to ka jira ganin ‘injera’, wani burodi mai dan tsami a tare da duk abincin da za a ci.

Yana da dandano mai dadi, madalla ga hanyar gasa burodi ta gargajiya da ke tabbatar da ba a rasa burodi sabon yi a ko yaushe, har ma a yankunan da ke da nisa a kasar.

“A Ethiopia, kowa ya san yadda ake gasa burodi, ta hanyar zamani ko ta gargajiya,” Beza Meseret, wata ‘yar kasar ta Gabashin Afirka, ta fada wa TRT Afrika. “Burodi na da matukar muhimmanci ga rayuwarmu kamar al’adunm da muka gada ne.”

A yayin da ake kallon abinci bai cika ba idan babu injera, Ethiopia a tarihi ta sha gwagwarmayar neman tsaya wa da kafafunta wajen samar da babban abinci na farko - alkama.

“Ethiopia “Ethiopia na kashe kusan dala biliyan daya a kowacce shekara don shigo da alkama domin biyan bukatar cikin gida, saboda noman da ake yi ba ya isa,” in ji wani rahoto da aka fitar daga ofishin Firaminista Abiy Ahmed.

Bayan shiga ofis a 2018, mutumin da ya lashe kambin Nobel peace na zaman lafiya ya fara gagarumin aiki na habaka samar da alkama a kasar.

A wajen Taron Afirka na 2025 a watan da ya gabata, ya kira matakin da “kasada” da ta haifar da da mai ido.

“A shekaru biyar da suka gabata, mun ninka kasar da muke nomawa, mun kara yawan kayan abincin da ake samarwa da kusan tan miliyan.

Alkama ce kashi 40 na wannan noma,” Firaminista Ahmed ya fada wa taron Tarayyar Afirka a Addis Ababa.

Bank. Shirin Bunkasa Noman Alkama na Ahmed ya samu habaka da zuba jarin dala miliyan 94, mafi yawa daga Bankin Cigaban Afirka.

An gudanar da wannan bangaren bankin me kula da Fasaha don Sauya Ayyukan Noma a Afirka (TAAT), wanda ke da manufar taimaka wa wajen bunkasa ayyukan noman nahiyar ta hanyar amfani da amfani da manyan fasaha.

Daga cikin kasashe 27 da aka zaba za su ci moriyar shirin, Kenya, Zambia, Zimbabwe, Nijeriya da Ethiopia ne aka bayyana za su samar da alkama.

“A shekaru uku da suka gabata, Shirin TAAT ya hada kai da gwamnatin Ethiopia da kamfanonin samar da iri don samar da nau’ikan alkama daban-daban ga manoman kasar, musamman a yankin da ba a samun zafi sosai da yake rage samun alkamar sosai,” in ji ofishin sashen na Bankin Cigaban Afirka.

Yankunan Afar, Amhara, Oromia da Somali da ke Ethiopia ne yankunan da ake samar da alkamar.

Shirin na da manufar amfanar da mutane miliyan 2.3, kashi 50 daga cikin su mata ne, wanda zai kara kudaden a ake samu a cikin gida, samar da ayyukan yi da damarmakin sana’o’i, da karfafa samar da abinci da cimaka.

Hanyar dogaro da kai

Ana shuka sabon irin alkamar da aka samar sau biyu a shekara, inda na biyun ba ya daukar lokaci sosai.

A tsakanin 2022 da 2023, kasar ta samar da tan miliyan 15.1 na alkama a hekta miliyan 4.18.

“Daga cikin wadannan, hekta miliyan 1.33 wani bangare ne na tsarin noman rani na musamman inda shukar da aka yi a waje mai girman hekta miliyan 2.85 kuma ya zama na noman damina da rani da aka saba noma a cikin su,” Bileme Seyoum, kakakin ofishin Firaministan Ethiopia, ta fada wa TRT Afrika.

Ya zuwa 2023/24, amfanin da ake samu ya karu da tan miliyan 23 na alkama inda adadin gonakin da ake noma wa ya karu zuwa hekta miliyan 6.58.

Adadin hekta miliyan 2.97 wani bangare ne na noman rani da aka ware, inda hekta miliyan 3.61 kuma aka ware ta don noma a lokacin da aka saba yi na rani da damuna.

Alkaluma daga ma’aikatar ayyukan noma ta Ethiopia sun nuna cewa kimanin manoma miliyan 3.4 ne suka shiga aikin noman alkama d arani a 2023-24, wanda Seyoum ta ce “na nuni ga muhimmancin zuba jari a wannan fanni”.

A 2024/2025, kasar ta so ta fadada kasar noman alkama zuwa hekta miliyan 8.37, wanda daga ciki hekta miliyan 4.27 zai zama karkashin noman rani inda hekta miliyan 4.1 kuma zai zama na noman alkama da aka saba yi.

Kalubale a kan hanya

A yayin da kasar ke gwagwarmayar cim ma dogaro da kai na noma, ta kuma fuskanci kalubalen jin kai.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa Ethiopia ta zama “daya daga cikin yankunan a yunwa ke addaba a duniya saboda rikici, raba mutane da matsugunansu da munin yanayi”.

“Jimillar mutane miliyan 5.5, wadand amiliyan 1.7 daga ciki mutane ne da aka raba da matsugunansu, na fama da karancin abinci,” in ji WFP a shafinta na yanar gizo.

Sanarwar ta ambaci cewa kasar “na bukatar dala miliyan 338 don co gaba da taimaka wa marasa galihu da masu rauni da ke Ethiopia nan da watan Mayun 2025.”

A yayin da take bayyana cewa bukatar neman dogaro da kai a samar da alkama da abinci “babban kalubale ne da ke bukatar mafita”, in ji ofishin Firaministan, yana mai cewa kasar ta dauki niyyar cimma wannan manufa.

“A lokacin da muka ce Ethiopia na da isasshiyar alkama, muna nufin kasar ba za ta sake dogaro kan shigo da alkama daga kasashen waje ba saboda noma ta sosai a ‘yan kwanakin nan. Sakamakon haka, an kawar da bukatar shigo da alkama. Ethiopia ta daina shigo da alkama gaba daya daga kasashen waje.”

TUSHEN:TRT Afrika
Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us