Daga Millicent Akeyo da Sylvia Chebet
Afirka ta Kudu na guna-guni ga abin da ta kira da zalunci daga Amurka bayan Shugaba Donald Trump ya sake tayar da tsohon fami ta hanyar kira da a kalubalanci dokar kasar kan mallakar filaye da gonaki.
"Munanan abubuwa na faruwa a Afirka ta Kudu," zargin da Trump ya yi na baya bayan nan. "Suna kwace gonaki da filaye, suna karbe gonaki, watakila ma suna yin abin da ya fi wannan muni."
Afirka ta Kudu ta kalubalanci wannan mataki da babbar murya. "Ba za a zalunce mu ba," in ji Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Kakakin shugaban kasar Vincent Bagwenya, ya yi karin haske cewa Afirka ta Kudu ba ta da dokar da ke nuna wariyar launin fata.
"Dukkan dokokinmu na daukar haske ne daga kundin tsarin mulki," in ji shi, yana mai jaddada cewa dokar mallakar kasar na da manufar kawar da bambancin launi wajen mallakar kasa da yake da tarihi, ba wai doka ce ta kwace wa wasu gonaki ba.
Kuskure a tarihi
Batun mallakar kasa a Afirka ta Kudu abu ne da aka kwashe shekaru da dama ana cikin takaici a kansa.
A 1913, 'yan mulkin mallaka na Birtaniya sun hana bakaken fatar Afirka ta Kudu mallakar gonaki ko ba su wani bangare na gonaki, a wani tsari na hana su mallakar kadara da nuna wariya.
Mai fafutuka Tembeka Ngcukaitobi ya ce "Mulkin farar fata tsiraru ba tsarin siyasa ba ne kawai, ya haifar da tsarin tattalin arziki na hana bakar fata mallakar komai."
Alkaluma na bayyana wannan gaskiya mai daci. Manoma farar fata, da ba su wuce kashi 8 na jama'ar Afirka ta Kudu miliyan 63 ba, su suka mallaki kimanin kashi uku cikin hudu na kasar.
Wannan lamari bai sauya ba tun bayan kawo karshen mulkin farar fata tsiraru.
A watan Janairun nan, Shugaba Ramaphosa ya sanya hannu kan Dokar Mallakin Kasa da ta bai wa gwamnati damar karbe gonakin mutane - ciki har da biyan diyya - idan lamarin ya zama "na adalci da daidaito kuma wanda jama'a ke so".
Malamin jami'a kuma mai nazari Ongema Mtimka ya yi amanna cewa Trump ya yi kuskuren dirar wa Afirka ta Kudu. Ya ce wannan ba wani abu ba ne illa tsagwaron siyasa.
"Mun san cewa Afirka ta Kudu na da manufar kasashen waje da Amurka ba ta so a 'yan shekarun nan, farawa da yakin Rasha da Ukraine, kai Isra'ila kara Kotun Kasa da Kasa, da kuma ayyukanta a kawancen BRICS. Gwamnatin Trump na kallon wadannan a matsayin abubuwan da ba za su lamunta ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Dokar da ta kawo rudani
A yayin da sabuwar doka ke da manufa ta musamman, ra'ayi ya bambanta a Afirka ta Kudu kan niyyar gwamnati ta aiwatar da ita.
Kallie Kriel, wanda ke jagorantar Kungiyar AfriForum da ke kare muradun 'yan Afirka farar fata ya ce da ma ana sa ran ganin matakan na Trump bayan an samar da dokar mallakar kasar.
"Ba ka bukatar zama masanin tattalin arziki kafin ka fahimci cewa idan ka karya dokar mallakar kasa, hakan zai tsoratar da masu zuba jari tare da korar su.
"Hakan zai kirkiri makiya a cikin kasa da suke tunani sosai game da kasuwanci marar tsangwama. Wannan ne abin da ya faru a lokacin da Shugaba Ramaphosa ya sanya hannu kan Dokar Mallakar Kasar," in ji shi.
Madugun 'Yan Adawa a Afirka ta Kudu, John Hlophe na Jam'iyyar MK, ya zargi AfriForum da cutar da muradun kasar ta hanyar yada bayanan karya a kasashen waje.
"An aikata cin amanar kasa... suna cin dunduniyar gwamnatinmu," in ji shi.
"Da fari dai, sun yi karya da cewa ana kwace gonakinsu... ana kashe su, ana kwace filayensu, wanda ba gaskiya ba ne. To, duba da wadannan karerayi da juya yadda zance yake, sai Trump ya fitar da umarnin cusguna wa Afirka ta Kudu."
Batun neman mafaka
Baya ga barazanar dakatar da bayar da tallafin kudade ga Afirka ta Kudu, gwamnatin Trump ta ce za ta bayar da mafaka irin ta 'yan gudun hijira ga fafaren fatar Afirka ta Kudu.
Martanin da kungiyoyin da ke wakiltar fararen fata 'yan tsiraru na Afirka ta Kudu shi ne "Godiya da yawa, amma ba ma so, mun gode."
Gwagwarmayar Orania da ke kare muradun fararen fatar Afirka ta Kudu, na kallon wannan matakin na Amurka a matsayin abin da ba a bukata.
"Martanin da muka mayar ga wannan a bayyane yake karara," kungiyar ta fada wa TRT Afrika.
"Mun yi amanna da cewa fararen fatar 'yan asalin Afirka ne; mu 'yan Afirka ne. Ba ma son zama tsiraru da aka bai wa mafaka a wata kasa mallakin wani daban."
Kriel na AfriForum ya yi watsi da tunanin a ba wa fararen fatar Afirka ta Kudu matsayin masu neman mafaka a Amurka.
"Ba ma son komawa wani waje. Ba za mu fada wa 'yan'yanmu su tafi wata kasa daban ba. Gaskiyar ita ce, kakanninmu sun yi aiki tukuru don tabbatar da cewa, mun wanzu da zama wani bangare na Afirka. Ba za mu ci zarafin wannan ba."
Bin diddigi
Kamar yadda tsananin sukar da Trump ke yi wa Afirka ta kudu ya ja hankalin kasashen duniya, sauran kasashe da ke da irin wannan matsala ta rashin daidaito da adalci na kallo da bin diddigin yadda lamarin na kawo sauyi a mallakar kasa da filaye ke tafiya.
Gwamnati ta jaddada cewa sabuwar dokar ta dace da dokokin kasa da kasa na mallakin kadarori inda take kuma magance daidaikun kalubalen cikin gida.
"Za mu yi magana da murya daya don kare muradun kasarmu, da dimokuradiyyar kundin tsarin mulkinmu. Ta hanyar tsayawa kan akidunmu, amfani da karfin albarkatunmu, da samar da manufar bai daya, za mu iya sauya wadannan yanayi na jarrabawa don cim ma burinmu." in ji Shugaba Ramaphosa a sanarwar da ya fitar a hukumance."
Wasu za su ce sukar Trump na iya yin abin da sulhun shekaru da dama bai iya yi ba - na hada kan jama'ar Afirka ta Kudu wajen kare manufofinsu na kasa.
A yayin da Afirka ta Kudu ke aikin tattare da wannan gamayyar ta tsofaffin ciwukan damuwa da sabuwar siyasa, duniya na kallon ko gyara wannan yanayi na mallakin kasa zai warkar da raunin da aka yi ba tare da samar da wasu sabbin ciwukan ba.