Sauyin yanayi: Yadda Sudan ta Kudu za ta ci moriyar nau'in Kofinta na Excelsa a duniya
Afirka
3 minti karatu
Sauyin yanayi: Yadda Sudan ta Kudu za ta ci moriyar nau'in Kofinta na Excelsa a duniyaMasana sun ce sai ana yawan amfani tare da nuna buƙatar nau’in Excelsa sosai za a iya cike gibin da ake samu na kofi a kasuwa sakamakon sauyin yanayi.
South Sudan coffee
4 Mars 2025

An gano nau’in kofi na Excelsa sama da shekaru ɗari da suka gabata a Sudan ta Kudu, kana kofin na samar da sabbin damammakin kasuwanci ga ‘yan kasar tare da janyo hankalin kasashen duniya sakamakon yanayin da ake ciki na rikicin kofi da sauyin yanayi ya haifar a duniya.

A yayin da manyan kasashe waɗanda ke samar da kofi ke fuskantar matsalar noma samakon rashin ruwa da sauyin yanayi da kuma farashi da ya yi tashin gwauron zabi da aka taba gani a tsawon shekaru, masana’antar ta tsunduma  neman mafita.

Masana sun yi kiyasin cewa noman kofi na bana a Brazil wadda ke fama da matsalar fari, kana ta ke kan gaba a duniya wajen noma Kofi, na iya raguwa da kusan kashi 12 cikin 100.

‘’Abin da tarihi ya nuna mana shi ne, wasu lokutan duniya ba ta baka zabi, kuma a halin da ake ciki, akwai manomam kofi da dama wadanda ke  fuskantar illar matsalar sauyin yanayi’’ a cewar shugaban sashen binciken Kofi na Royal Botanic Gardens, Kew a Landan.

Nau'in da ke jure cututtuka

'Yan asalin Sudan ta Kudu da wasu tsirarun ‘yan wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Kongo da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Uganda, suna noman nau’in kofin Excelsa, sai kuma kasashen Indiya, da Indonesia, da kuma Vietnam.

Tushen bishiyar da ganyanta masu kauri da kuma gangar jikinta mai girma ne suke bai wa nau’in ‘ya’yan kofi na Excelsa damar bunƙasa cikin yanayi mai tsanani, kamar fari da zafi fiye da sauran nau’in kofin.

Kazalika yana iya jure illar kwari da sauran cututtuka masu yawa da ke shafar kofi.

Sai dai duk da haka nau’in na ƙasa da 1 kashi daya a kasuwar duniya, idan aka kwatanta da kofin Arabica da Robusta waɗanda aka fi kasuwancinsu a duniya.  

Masan sun ce sai an nuna cewa ana amfani tare da bukatar nau’in Excelsa sosai don cike gibin da ake samu a kasuwa sakamakon sauyin yanayi.

Tsawon bishiyoyin Excelsa na iya kaiwa mita 15 (kimanin taku 49) sai dai ana iya sare ta don sauƙaƙa yin girbi.

Kofi da aka yi daga nau’in excelsa yana da ɗanɗano mai daɗi -ba kamar robusta ba—wand aktare da bayanin cakulan, 'ya'yan itatuwa masu duhu, da gyadan hazelnut. Sanna ya fi kama da nau’in kofi na arabica, sai dai ba shi da ɗaci .

Darajar miliyoyin daloli

"Babu wasu bayanai masu yawa akan wannan kofin da ke sahun gaba a yanzu, muna kara samun ilimi akansa a kullum,’’ kamar yadda Ian Paterson, manajan darekta na Equatoria Teak, wani kamfanin ayyukan noma da gandun daji wanda ke aiki a ƙasar sama da shekaru goma ya bayyana.

Kamfanin ya shafe tsawon shekaru da dama yana gudanar da binkice kan nau’in excelsa.

Sakamakon rahoton kamfanin na farko ya ba da kwarin gwiwa, inda bishiyoyin suka iya jure zafi fiye da sauran nau'in da ake da su. Kazalika kamfanin aiki tare da al'ummomi don farfado da masana'antar kofi da kuma fadada samuwarsa.

Yawancin bishiyoyi sun fara ‘ya’ya ne a kafon farko a wannan shekarar, kuma Paterson ya ce yana fatan fitar da kashi na farko na tan 7 zuwa manyan kantuna na musamman a Turai.

Zuwa shekarar 2027, nau’in kofin na iya samar da dala miliyan 2 a tattalin arzikin Sudan ta Kudu, inda aka samu manyan masu siye irin su Nespresso da suka nuna sha'awa.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us