Yadda Uganda ta samar wa sojoji gurbi a Majalisar Dokoki
Siyasa
5 minti karatu
Yadda Uganda ta samar wa sojoji gurbi a Majalisar DokokiTsarin majalisar dokokin Uganda na musamman ne saboda yadda kundin tsarin mulki ya tanadi kujeru 10 ga rundunar sojin kasar, tsarin da aka kaddamar a 1995 don shigar da sojoji shugabancin farar hula.
Uganda na da wakilcin sojoiji a majalisar dokoki bisa tanadin kundin tsarin mulki. / Hoto: Reuters
19 فبراير 2025

Uganda, kasar Gabashin Afirka mai mutane miliyan 48.6 da ke da tarihi, na da wani tsarin gudanarwar majalisar dokoki da ya bambanta shi da na sauran kasashe kuma yake na musamman.

Na farko shi ne ma yawan kujerunta. Majalisar dokokin na da kusan mambobi 556, kusan ninkin ukun na kasashe makotanta irin su Burundi da Rwanda.

Amma abin da ya sa ta ma fi zama ta daban a shuganacin Afirka shi ne - wanzuwar wakilan rundunar soji a matsayin masu yin dokoki da kuma karfin fada a ji a jagoranci.

Wanzuwar sojoji a majalisar dokoki a tasarin dimokuradiyya ba ya kawo wani rashin jin dadi ko tarnaki a kasa.

Sabanin haka ma, mafi yawan 'yan majalisa na murna da alfaharin kasancewa wani bangare na wannan tsari.

"A lokacin da Sojojin Tirjiya na Kasa (Reshen Soji na Gwagwarmayar Tirjiya ta Kasa) suka karbe mulki a 1986, shugaban lokacin ya yi tunani biyu na baiwa sojoji damar zama wani bangare na shugabancin farar hula," in ji Linos Ngompek, dan majalisa kuma shugaban kwamitin tsaro da harkokin cikin gida.

"Manufar hakan ita ce a baiwa sojoji damar fahimtar yadda shugabancin farar hula yake aiki."

Gamayya mai dalili

Uganda ta kasance daya daga cikin 'yan kasashe a duniya da suka amince da wakilci a majalisar dokoki a matakai daban-daban na siyasa.

Duk da cewa dai falsafar wadanna tsare-tsare sun sha bamban.

Dakarun Tsaron Jama'a na Uganda (UPDF) na da wakilci a majalisar dokoki tun 1995, a lokacin da sabon kundin tsarin mulkin kasar ya bayar da damar hakan.

Manufar ita ce a shigar da sojoji cikin harkokin mulki don tabbatar da biyayyar su ga farar hula karkashin mulkin Yoweri Museveni, wanda ya hau mulki karkashin gwagwarmayar sojoji a 1986.

'Yan majalisa sojoji na bayar da gudunmawar kwarewarsu ga sha'anin tsaro. Hoto: Reuters

Manufar wannan hadaka ta fi mayar da hankali kan muhimmancin rawar da sojoji ke taka wa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa.

"Wakilcin UPDF a majalisar dokokin Uganda na taimaka musu wajen fahimtar yanayi da siyasar kasar, ta hanyar shiga siyasa da fahimtar ya ma kasar ke tafiya da yadda ake yin dokoki da kuma bayar da shawarwari kan sha'anin tsaron kasa," in ji dan majalisa Ngompek, a tattaunawar da ya yi da TRT Afrika.

Duba ga tarihin rikici da juyin mulki a Uganda, masu nazari da dama na bayyana shigar da sojoji cikin majalisar dokokin na samar da zaman lafiya siyasa da ta al'umma a kasar.

Mambobin majalisar dokokin ,asu kakin soja na bayar da gudunmawar kwarewarsu kan batutuwan tsaro, suna tabbatar da kwararan matakan manufofin tsaro da kasafin soji.

Shigar su cikin gwamnati na ba wa sojojin damar shiga kai tsaye cikin ayyukan tsara manufofin kasa.

"Kasancewar su wani bangare na majalisar dokoki na taimaka mana don tabbatar da zaman lafiyar siyasa.

Kowanne irin mataki majalisa ta dauka, ana sanar da UPDF, da ma shugabancin rundunar sojin kasa. Sannan sai su dauki mataki duba ga siyasar kasar," in ji Ngompek.

Tsare-Tsare mabambanta

Tunanin wanzuwar sojoji a harkokin farar hula na yawan janyo ka-ce-na-ce.

A yayin da kasashe irin su Ethiopia da Somalia ke gabatar da wanzuwar sojoji a bainar jama'a, sauran kasashen irin su Kenya da Tanzania na yin abu na bambance soji da farar hula. A kasashen biyu, ganin sojoji na bayyana alamun rikici.

Uganda ta zama ta musamman saboda wakilcin sojoji a majalisar dokokinta, inda aka ba wa sojojin kujeru 10 da su suke zabar su.

Tun 1995 Rundunar Sojin Uganda ke da wakilci a majalisar dokoki ta kasa . Hoto: Reuters

Sauran kasashen Afirka na da matakai daban-daban na yadda sojoji suke da iko a gwamnati, ciki har da Burkina Faso, Sudan da Mali, wadanda suke da shugabannin soji ko majalisun mika mulki inda sojoji suke rike da madafun iko.

Sannan sai Masar, wadda sojojinta ke da karfin fada a ji a shugabancin kasar amma ba tare da wakilci a majalisar dokoki ba.

Sojojin Zimbabwe na taka rawa sosai a shugabanci amma ba ta hanyar aiki da majalisar dokoki ba.

Aminta a cikin majalisa

A baya bayan nan, wasu 'yan majalisa sun bayar da shawara cewa ya kamata mambobin majalisar da ke wakiltar sojoji si cire kaki a lokacin zaman majalisa, suna masu kawo dalilan yanayin da sojojin ke ciki. Sai dai kuma, sauran sun yi watsi da wannan shawara, inda mafi yawan 'yan majalisa ke cewa wannan tsari ya yi musu daidai.

Ngompek na da ra'ayin cewa sojoji su ci gaba da sanya kayan sarki har ma a zauren majalisar dokokin yayin zama.

"Wannan ne abin da ke fayyace su waye sojoji da UPDF. Sojoji ba za su iya zuwa majalisar dokoki da farin kaya ba.

"Tun da dai suna wakiltar UPDF ne. dole su saka kayan sarki, kamar yadda doka ta tanada. Kuma wannan ne kayan ado da yaki na soji," ya fada wa TRT Afrika.

Kasancewar sojoji a cikin majalisar dokoki na ci gaba da janyo martani daban-daban. Ko ma dai wannan batu na da amfani ko akasin haka, batu ne na ra'ayi, wanda tarihi da al'adu ke fayyacewa.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us