NIJERIYA
2 minti karatu
Masu son yi wa Sanata Natasha kiranye ba su bi ka’ida ba -INEC
Hukumar zaɓe ta Nijeriya ta fitar da sanarwa kan yunƙurin da wasu ke yi na yi wa sanatar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti, inda ta ce ta jingine shirin har sai ta samu cikakkun bayanai daga masu buƙatar kiranyen.
Masu son yi wa Sanata Natasha kiranye ba su bi ka’ida ba -INEC
/ Others
25 Maris 2025

Hukumar zaɓe ta Nijeriya, INEC ta ce ta jingine batun kiranyen da wasu ke son yi wa Sanatar jihar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti, sakamakon rashin cikakkun bayanai daga masu shigar da ƙorafin.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata 25 ga Maris, INEC ta ce ta karɓi tarin takardu cikin jakunkuna shida da aka ce suna ɗauke da sa-hannun mutanen da ke son yi wa sanatar kiranye.

An ce takardun suna ɗauke da sa-hannun sama da rabin masu rijistar yin zaɓe a yankin, wato rabin jimillar mutane 474,554 da ke rumfunan zaɓe 902 da ke mazaɓa 57 a ƙananan hukumomi biyar, Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene.

Sai dai hukumar ta ce ta lura da cewa wakilan masu kai ƙorafin ba su bayar da adireshinsu ba, da lambar waya, da adireshin imel, a kan wasiƙar da ta zo tare da ƙorafin nasu, ta yadda za a iya tuntuɓar su.

INEC ta ce dokar zaɓe na buƙatar waɗannan cikakkun bayanai, ba iya abin da suka ruboto ba, wato adirsehin “Okene, Jihar Kogi”, wanda ba takamaiman adireshi ba ne da za a iya tuntuɓar wakilan.

A cewar sanarwar, “Lambar babban mai shigar da ƙorafi shi kaɗai aka kawo, saɓanin lambobin duka sauran wakilan masu ƙorafin. Amma dai INEC ta ce za ta duba wasu hanyoyin tuntuɓar masu ƙorafin kan halin da ake ciki.

Cika sharuɗa

Haka nan hukumar ta jaddada cewa masu zaɓe a gundumar waɗanda suka sa-hannu kan ƙarafin su kaɗai ke da alhakin yin kiranyen, kuma su za su tabbatar da cewa sun fid da tsammani daga sanatar da ke wakiltar su.

INEC ta ce da zarar ƙorafin ya cika sharuɗɗan gabatar da buƙata, hukumar za ta fara aikin tantance sa-hannun mutanen a duka mazaɓun yankin, inda za a gayyaci masu rijistar zaɓe da suka saka hannu a bainar jama’a.

Sannan masu ƙorafin da kuma wadda ake son yi wa kiranyen suna da ‘yancin ba da wakilai da za su saka ido kan tantancewar. Haka ma masu saka-ido daga ‘yan jarida za su iya turo nasu wakilan.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us