KASUWANCI
4 minti karatu
Kasuwancin duniya ya faɗa matsala saboda rikicin Amurka da China, ana iya shiga mummunan yanayi: WTO
A farkon shekara, WTO ta sa ran ganin kasuwanci ya habaka a 2025 da 2026, tare da habakar shiga da fitar da kayayyaki duba ga kudaden da ake samu a duniya, kasuwanci na habaka cikin sauri sosai, amma alkaluman da aka sake nazari sun nesanta da haka.
Kasuwancin duniya ya faɗa matsala saboda rikicin Amurka da China, ana iya shiga mummunan yanayi: WTO
A yayin da kasuwancin Amurka da China bai wuce kashei uku na kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki a duniya ba, Okonji-Iweala ta yi gargadin cewa rabuwar su da juna “na iya zuwa da sakamako marar dadi sosai”. / AP
16 Afrilu 2025

Ana tsammanin durkushewar harkokin kasuwanci a duniya a wannan shekarar saboda yadda Shugaba Trump ya kara haraji, wanda ya kawo rashin tabbas da ke barazanan kawo “mummunan halin tsanani” ga duniya, in ji gargadin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya.

Tun bayan dawo wa kan mulki, trump ya kakaba karin kashi 10 na haraji kan kayayyakin da ake shigarwa kasar daga sassan duniya inda aka saka kashi 25 kan fari da bakin karfe da motocin hawa.

A yayin da Trump ya dakatar da karin harajin kan wasu kasashe, amma ya kara ta’azzara rikici da China, inda ya saka harajin kashi 145 kan kayan da ake shigar da su Amurka daga China, inda China kuma ta mayar da martani da saka harajin kashi 125 kan kayan da ake kai musu dag Amurka

“Ina da matukar damuwa game da rashin tabbas din da ke tattare da manufar kasuwanci, ciki har da rikicin Amurka da China,” in ji Shugabar WTO Ngozi Okonjp-Iweal a wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba.

“Lafawar rikicin a baya bayan nan ya dan saukaka wasu matsin lambar da ke addabar kasuwancin duniya,” in ji ta.

“Sai dai kuma, rashin tabbas din da ake fuskanta na zama barazanar hana bunkasar duniya, tare da mummunan sakamako mai tsanani ga duniya, musamman ga kasashen da ba su da tattalin arziki mai karfi.”

A farkon shekara, WTO ta sa ran ganin kasuwanci ya habaka a 2025 da 2026, tare da habakar shiga da fitar da kayayyaki duba ga kudaden da ake samu a duniya, kasuwanci na habaka cikin sauri sosai.

Amma a rahoton shekara na kasuwancin duniya da kungiyar ta fitar a ranar Laraba, an bayyana a yadda abubuw ake tafiya a yanzu haka, kasuwancin shigarwa da fitar da kayayyaki na kan faduwa da kashi 0.2 a wannan shekarar.

Adadin, da aka tattara duba ga yanayin haraji a 14 ga Afrilu, ta kai kusan kashi uku kasa da abinda aka yi hasashen gani ba tare da harajin a Turmp ya saka wa kasashen duniya ba.

'Matsananciyar raguwa mai hatsari'

WTO ta yi gargadi cewa za a iya samun “matsananciyar raguwa mai hatsari” da za ta janyo “karin karyewar kasuwanci, zuwa kashi 1.5 a 2025, idan lamarin ya munana.”

WTO din ta kuma ja hankali cewa kasuwancin ayyuka, wanda kai tsaye harajin bai shafe shi ba, ana “sa ran zai illatu shi ma”.

Kasuwancin ayyuka a fadin duniya zai habaka da kashi 4.0 - adadin da yake kasa da yadda aka yi hasashe.

A bana, ana s aran tasirin harajin zai shafi yankuna da dama, in ji WTO.

“A karkashin manufofin da ake da su a yau, ana sa ran Arewacin Amurka zia samu tawaya da kashi 12.6 wajen fitar da kayayyaki da kashi 9.6 wajen shigar da kayayyaki a 2025,” in ji kungiyar.

“Kokarin yankin zai samu nakasun kashi 1.7 a 2025 a kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki a duniya,” hukumar ta kara bayyanawa.

Asiya, ana sa mata ran samun “‘yar habaka”, inda shiga d fitar da kayayyakin za su habaka da kashi 1.6.

Fitar da kayayyaki daga Turai kuma zai habaka da kashi daya, shigar da su kuma da kashi 1.9.

'Rabuwa da juna'

Okonjo-Iweala ta fada wa manema labarai cewa ta damu matuka game da “Raguwa ta nan da dan a kasuwancin Amurka da China”, wanda a yanzu ake sa ran zai ragu da kashi 81.

“Wannan matakin raguwar na kasuwancin Amurka da China da muke magana a kai, na iya raba tattalin arzikin biyu da juna,” in ji ta.

A yayin da kasuwancin Amurka da China bai wuce kashei uku na kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki a duniya ba, Okonji-Iweala ta yi gargadin cewa rabuwar su da juna “na iya zuwa da sakamako marar dadi sosai”.

Ta bayyana damuwar cewa hakan na iya “bayar d agudunmawa wajen kacalcala tattalin arzikin duniya tare da samar da bangarori biyu da suke rabe da juna”.

A wannan yanayi, “hasashenmu na bayyana cewa kudaden da ake samu a duniya za su ragu da kusan kashi bakwai a tsawon lokaci,” in ji ta.

“Wannan na da muhimmancin a kalle shi.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us