DUNIYA
2 minti karatu
An kashe mutane da dama yayin da RSF ta yi luguden wuta a Al Fasher ta Sudan
Tun daga watan Mayu ake gwabza yaƙi a Al Fasher, wata babbar cibiyar agaji
An kashe mutane da dama yayin da RSF ta yi luguden wuta a Al Fasher ta Sudan
The army said its forces responded to the RSF attacks on the city, killing 70 militants, injuring dozens, and destroying 15 combat vehicles and two fuel tankers. / AP
17 Afrilu 2025

Aƙalla fararen hula ‘yan Sudan 62 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 75 suka jikkata a harin bama-baman da dakarun RSF suka kai a Al Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, in ji sojojin kasar.

Sanarwar soji ta bayyana a ranar Alhamis cewa mata 17 da yara 15 na cikin wadanda suka mutu a harin da aka kai na kan mai uwa da wabi a birnin.

Sojojin sun ce sun mayar da martani ga hare-haren RSF a birnin, inda suka kashe mayaka 70, suka jikkata wasu da dama, tare da lalata motocin yaki 15 da tankunan mai guda biyu.

Babu wani karin bayani daga ɓangaren 'yan tawayen game da wannan sanarwar ta sojoji.

Matsalar samar a agajin kin kai

Al Fasher ta sha fama da rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar asarar rayuka tsakanin sojojin Sudan da RSF tun watan Mayu 2024, duk da gargaɗin da ƙasashen duniya ke yi kan haɗarin yaƙi a birnin, wanda ke zama cibiyar ayyukan jin kai a dukkan jihohin Darfur guda biyar.

A farkon wannan makon, RSF ta yi iƙirarin cewa ta karɓe iko da sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam da ke Al Fasher, bayan wata arangama da sojojin gwamnati.

Aƙalla fararen hula 400 sun mutu, yayin da kusan mutum 400,000 suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin, a cewar alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tun daga ranar 15 ga Afrilun 2023, RSF ke gwabza faɗa da sojojin Sudan domin neman iko da ƙasar, abin da ya haifar da dubban mace-mace a ɗaya daga cikin mafi munin rikicin jin ƙai a duniya.

Fiye da mutane 20,000 ne suka mutu, yayin da mutum miliyan 15 suka rasa matsugunansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin cikin gida. Sai dai binciken wasu masana daga Amurka ya ƙiyasta adadin waɗanda suka mutu ya kai kusan 130,000.

A makonnin baya-bayan nan, RSF ta rasa manyan yankuna da dama a faɗin Sudan ga sojojin gwamnati.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us