WASANNI
2 minti karatu
Klopp ya amince ya tattauna don kama aiki a Real Madrid
Tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp zai fara tattauna da Real Madrid don maye gurbin Carlo Ancelotti a ƙarshen kakar bana.
Klopp ya amince ya tattauna don kama aiki a Real Madrid
/ AFP
17 Afrilu 2025

Gwarzon tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya amince ya tattauna da wakilan Real Madrid domin komawa horar da ƙungiyar, inda zai maye gurbin Carlo Ancelotti.

Tun a bazarar bara ne Jurgen Klopp ya ajiye aikin horar da ƙungiyar ƙwallo, inda ya bar tawagar Liverpool ta Ingila wadda ya yi shekara takwas yana horarwa.

Sai dai akwai yiwuwar zai koma fagen fama a Real Madrid ta Sifaniya a ƙarshen kakar bana, yayin da rahotanni ke cewa Klopp ya amince ya tattauna kan kwantiragin kama aiki a Madrid.

Wannan labarin na zuwa ne yayin da aka yi waje da Real Madrid daga gasar Zakarun Turai, bayan Arsenal ta Ingila ta doke su da jimillar ƙwallaye 5-1 cikin wasann biyu a gida da waje.

A yanzu alamu na nuna cewa Madrid za ta yi hannun riga da kocinta Carlo Ancelotti a ƙarshen kakar 2024/25. Ƙungiyar na neman wanda zai karɓi ragama, kuma Klopp na kangaba.

Shafin Goal ya ambato shafin UOL na cewa Jurgen Klopp yana da aniyar fara tattaunawa da Real Madrid tun yanzu.

Tafiyar Ancelotti

A halin yanzu, Klopp mai shekaru 57 yana riƙe da muƙamin daraktan wasanni a Gamayyar Kamfanin Red Bull, wanda yake da ƙungioyin ƙwallo a ƙasashe daban-daban.

Lokacin aikinsa a Liverpool, Klopp ya ci kofuna da dama ciki har da na Firimiya, da Zakarun Turai, da Super Cup, da Club World Cup, da FA Cup, da kuma kofin Carabao.

Shi kuwa kocin Madrid Carlo Ancelotti na yanzu ɗan asalin Italiya ne mai shekaru 65. Ya riƙe tawagar karo biyu, tsakanin 2013-15, da kuma daga 2021 zuwa yanzu.

Ya ciyo wa Real Madrid kofunan La Liga biyu, do na Zakarun Turai uku, da Copa del Rey uku, da Super Cups uku, da kuma Club World Cup biyu. Sai dai a yanzu Ancelotti yana fama da ƙalubale a kakar bana.

Real Madrid na bin Barcelona a teburin la Liga, da maki huɗu, sannan za su kara da Barcelona a wasan ƙarshe na kofin Copa del Rey.

Tuni Ancelotti ya amsa cewa akwai yiwuwar ya kama hanyar barin Madrid inda aka ambato shi yana cewa, “Zan iya [tafiya] wannan shekarar ko baɗi lokacin da kwantiraginta za ta ƙare... Ba wata matsala ba ce.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us