AFIRKA
1 minti karatu
Nijeriya ta ƙulla yarjejeniyar ma'adinai da Afirka ta Kudu
Nijeriya, wacce take da nau'in ma'adanai fiye da 20 da take da su a jibege da za a iya kasuwanci da su, ta sanya hannu kan yarjejeniyar ma'adanai da Afirka ta Kudu a ƙoƙarinta na raba ƙafa wajen samun kuɗaɗen shiga.
Nijeriya ta ƙulla yarjejeniyar ma'adinai da Afirka ta Kudu
Nigeria minerals / Reuters
17 Afrilu 2025

Nijeriya da Afirka ta Kudu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya don bunƙasa haɗin gwiwa a fannin haƙar ma'adinai, in ji ministan ma'adinai na Nijeriya a ranar Alhamis, inda ya bayyana yunƙurin Abuja na karkata tattalin arzikinta daga man fetur.

Ministan ma'adinai Dele Alake ya ce kasashen biyu za su yi hadin gwiwa a kan aikin hakar ma'adinai, da suka hada da taswirar kasa ta hanyar amfani da jirage marasa matuka, da raba bayanan ma'adinai, tare da yin bincike kan ma'adinan noma da makamashi a Nijeriya.

Baya ga man fetur, Nijeriya tana kuma da arzikin zinari da ma’adanan limsetone na yin sumunti da lithium da tama da zinc.

Nijeriya na da kusan ma'adinan 23 da yawansu ya kai na kasuwanci.

Nijeriya na neman sake farfado da fannin hakar ma'adinai da aka dade ba a samu ci gaba ba, wanda ke ba da gudunmawar kasa da kashi 1 cikin 100 na yawan amfanin da take samu a cikin gida.

Ƙwarewar Afirka ta Kudu a fannin ma’adanai ya sa ta zama babbar abokiyar haɗin gwiwa a wannan ƙoƙarin, in ji Alake.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us