TURKIYYA
4 minti karatu
Hana sanya ɗankwali na tauye haƙƙoƙin mata a duniya: in ji Sumeyye Erdogan Bayraktar
A lokacin da ake fuskantar daduwar Kyamar Musulunci, Sumeyye ta ce hana sanya kaya na addini kamar dankwali ko hijabi na nuna wariya ga mata Musulmai da kuma kirkirar ‘katangar karfe’ a bangarorin ilimi, wasanni, da ayyukan yi.
Hana sanya ɗankwali na tauye haƙƙoƙin mata a duniya: in ji Sumeyye Erdogan Bayraktar
Sumeyye Erdogan Bayraktar, 'yar Shugaban Kasar Turkiyya / AA
18 Afrilu 2025

Sumeyye Erdogan Bayraktar, Shugabar Kwamitin Amintattun KADEM (Kungiyar Mata da Dimokuradiyya), ta magantu kan daduwar nuna kyama ga Musulunci da wariyar da ake nuna wa mata masu riko da addini a duniya, musamman a kasashen Yamma.

Da take kawo misalin abubuwan da suka faru a baya bayan nan irin sy hana saka dankwali ko hijab da Faransa ta yi a cikin harkokin wasanni wanda ya janyo cece-ku-ce, Bayraktar ta la’anci abinda ta kira da “shirmammen mataki” da ke daukar siffar addini a matsayin wata alfarma da ake bai wa mutane bayan sun balaga.

Da take jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a Jami’ar Ibn Haldun, Bayraktar ta yi nuni ga wani yanayi mara dadi da ke faruwa: matan da ke sanya dankwali na shiga matsin lambar tirsasa su su sarayar da ‘yancin neman ilimi, aikin yi, ko shiga harkokin wasanni domin su yi biyayya ga addininsu.

“Wadannan manufofi na fitar da mata daga da’irar rayuwan jama’a, na saka katangar karfe da hna su amfana da ‘yancin da addininsu ya ba su,” in ji ta.

Da take kawo misali ga karatu a Turai, Bayraktar ta yi karin haske da cewa masu neman aiki da ke daura dankwali ba sa samun damar a kira su intabiyu da kashi 65.

“Kashi 40 na mata da ke saka dankwali a wuraren aiki na fuskantar nuna wariya,” ta fada. “Wannan ba iyakacin rayuwar aiki ta didsikun mutane ke illatawa ba, yana kuma ruguza kokarin samar da daidaito tsakanin mata da maza da adalcin zamantakewa.”

Aniyar KADEM ta tabbatar da zama tare da kare hakkoki

Bayraktar ta sake jaddada aniyar kungiyar ta kalubalantar kaskantar da rawar da mata ke takawa a cikin al’umma.

“Muna watsi da kakaba tsarin dole mata su saka kaya iri guda da ya samo asali daga zantuttukan zamantarwa,” in ji ta.

“Za mu ci gaba da neman baiwa mata ‘yancin addini, da ke bin ka’idojin yankunansu, al’adunsu da ma duba ga hakkoki.”

Ta jaddada muhimmancin baiwa mata ‘yancin rayuwa da yin ayyuka kamar yadadda addininsu ya tanada: “A lokacin da aka hana wannan ‘yanci, al’umma na shan wahala baki daya.

Duk al’ummar da ta cire mata daga tsarin rayuwarta to ba za ta iya kiran kanta mai tafiya da kowa, ko mai aiki da dimokuradiyya ba.”

Hanin da Faransa ta yi a wasanni: Alamun wanzuwa zurfafan matsaloli

Bayraktar ta yi kakkausan suka ga dalilan da ya sanya Faransa hana saka hijabi a yayin wasanni - wai “saboda siffar addini na raba kan al’umma.”

Ta kuma ce za a iya amfani da wannan tunani wajen hana bayyana duk wata irin siffa, ciki har da yare, kabila ko ma wasu dabi’u bayyanannu.

“Wannan ba batu ne na raba kasa da addini ba,” in ji ta. “Wannan batu ne na amfani da tsarin raba kasa da addini wajen bakantar da Musulunci.”

“Wannan yaki da ra’ayin al’uma ne”

Da take bayyana batun a matsayin wanda ya ma haura na nuna bambanci, Bayraktar ta ce “yaki da ra’yi da manufofin jama’a ne ta hanyoyi daban-daban” inda mata masu riƙo da addini, musamman Musulmai da ke sanya hijabi ko dankwali suke zama wadanda ake kai wa hari.

“Hoto guda daya a wajen neman aiki na iya goge komai da mace ta yi aiki don ta samu - kwarewarta, iliminta da gudunmawarta. Wannan tsananin rashin adalci ne,” in ji ta.

Kira ga daukar matakin ‘yanci ga kowa

“Wannan ba batu ne na ra’ayin addini ba,” in ji Bayraktar a karshen bayaninta. “Ya shafi ‘yancin wanzuwa, ‘yancin rayuwa, ‘yancin yin aiki, da ‘yancin tunani.”

Da take kira da a dauki matakin bai daya, ta yi alkawarin cewa “ba za mu sarayar da ‘yancinmu ba.

Za mu yi gwagwarmaya ga duniya da ta cika da bambance-bambance, take kuma da aniyar dabbaka daidito da adalci.”

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us