AFIRKA
2 minti karatu
Ministocin ƙasashen yankin Tafkin Chadi sun ƙaddamar da rigakafin cutar shan-inna na haɗin-gwiwa
Ministocin sun ƙaddamar da rigakafin cutar ne a daidai lokacin da wani sabon nau'i na cutar ke ƙara bazuwa.
Ministocin ƙasashen yankin Tafkin Chadi sun ƙaddamar da rigakafin cutar shan-inna na haɗin-gwiwa
Za a gudanar da aikin rigakafin cutar shan inna daga ranar 24 zuwa 28 ga Afrilu / Reuters
18 Afrilu 2025

Ministocin Kiwon Lafiya na ƙasashen Kamaru da Chadi da Nijar da ke yankin Tafkin Chadi sun ƙaddamar da wani shiri na rigakafin cutar shan-inna domin kare yara ‘yan ƙasa da shekaru 5 miliyan 83 daga kamuwa da cutar shan-inna iri ta biyu.

A cikin watanni 12 da suka gabata, an gano bambance-bambancen nau'in cutar shan-inna iri ta biyu a cikin muhalli (samfurin ruwan sha) da kuma tsakanin mutane a cikin ƙasashe hudu, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Za a gudanar da rigakafin cutar shan-inna daga ranar 24 zuwa 28 ga Afrilu, wanda ake sa ran gudanarwa ga mutanen da suka fi cikin hatsari da kuma jama’ar da ke nesa da gari.

An samu rahoton gano mutum 210 a dukkan ƙasashen hudu, 140 daga cikinsu sun samu shanyewar rabin jiki.

Ɗaukar cuta tsakanin ƙasa da ƙasa

“Yankin Tafkin Chadi ya kasance yanki mai muhimmanci a yaƙin da muke yi da cutar shan-inna. Ta hanyar haɗa kanmu a matsayinmu na yanki, za mu ci gaba da ƙarfafa aikin da muke yi domin kawo ƙarshen polio baki ɗaya,” in ji Ministan Lafiya na Chadi, Abdelmadjid Abderahim.

Hukumar ta WHO ta ce kusan ma'aikata miliyan 1.1 da ke bakin aiki, da suka haɗa da masu yin alluran rigakafi, masu wayar da kan jama'a da masu sa ido da sun shirya don tallafa wa aikin.

Duk da cewa ba a bayar da rahoton ɓullar cutar ba a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, WHO ta ce bincikenta ya yi nuni da barazanar da ke da akwai ta yaɗa cutar tsakanin ƙasashe da buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashe.

Fiye da kashi 50 cikin 100 na cutar shan-inna da aka ruwaito a Chadi a cikin 2024 suna da alaƙa da nau'in da ke yawo a Kamaru, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da aiki tare da ƙoƙarin magance cutar, in ji shi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us