Shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdourahmane Tiani, ya yi wani gagarumin sauyi ga gwamnatinsa a ranar Alhamis, 17 ga watan Afrilu, inda ya faɗaɗa majalisar ministocinsa zuwa mambobi 26, idan aka kwatanta da 23 a baya.
Waɗannan muhimman sauye-sauyen, waɗanda suka ƙunshi samar da sabbin ma’aikatu uku da kuma yin garambawul a ofisoshi da dama, sun kai ga naɗa sabbin ministoci takwas, ciki har da mambobin kwamitin da ya gudanar da taron ƙasa.
Daga cikinsu akwai Abdoulaye Seydou, wanda shi ne jagoran tafiyar M62, wanda a halin yanzu shi ne Ministan Kasuwanci da Masana’antu.
Haka kuma Ali Ben Sala Hamouda an ƙara masa girma zuwa Ministan Al’adu da Inganta Ɗabi’un Zamantakewa.
Daga ɓangaren waɗanda za su bar muƙaminsu, Ms Aïssa Laouan Wandarama da kuma Mista Mohamed Sidi Raliou, za su bar muƙamansu.
Sabbin ministocin da suka samu gurbi a gwamnatin Janar Tiani sun haɗa da Kanal Abdoulkadri Amadou Daouda wanda ya karɓi ragamar Ma’aikatar Tsara Birane da Gidaje.
Kazalika an naɗa Sidi Mohamed Al Mahmoud a matsayin Ministan Ma’aikatar Matasa da Wasanni.
Haka kuma malaman jami’o’i biyu masu muƙamin farfesa biyu sun zama ministoci.
Sun haɗa da Sidikou Ramatou Djermokoye Seyni wadda aka bai wa Ministar Ƙidaya da Farfesa Farmo Moumouni wanda ya zama Ministan Ilimi da Koyar da Sana’o’i.
Haka kuma Adji Ali Salatou shi ne sabon Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani.
Sai kuma Mahamane Sidi ya zama wakilin firaminista wanda zai mayar da hankali kan kasafin kuɗi.