NIJERIYA
2 minti karatu
Abu biyar da ministocin harkokin wajen Nijeriya da Nijar suka tattauna a kai
Daga cikin abubuwan da ministocin Nijeriya da Nijar suka tattauna har da batun gina babbar hanyar mota wadda za ta ratsa ta cikin sahara domin inganta sufuri a tsakanin ƙasashen.
Abu biyar da ministocin harkokin wajen Nijeriya da Nijar suka tattauna a kai
A tattaunawar da Yusuf Tuggar ya yi da takwaransa na Nijar Bakary Yaou Sangare, sun yi nazari kan irin ƙalubalen da ƙasashen ke fuskanta.
17 Afrilu 2025

Ministocin harkokin wajen Nijeriya da Nijar sun gudanar da wata tattaunawa game da tsaron kan iyaka da ta’addanci da haɗin kan tattalin arziki a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar tsakanin maƙwabtan biyu tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a watan Yulin 2023.

Wannan tattaunawar na zuwa ne bayan a watan nan Nijeriya ta ci gaba da kira ga gwamnatin Nijar ta saki Shugaba Mohamed Bazoum, wanda aka yi wa ɗaurin-talala a fadar shugaban ƙsasar ta Nijar.

Ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya kai Yamai ita ce ta biyu da wani babban jami’in Nijeriya ya kai ƙasar bayan juyin mulki a ƙasar inda a kwanakin baya babban hafsan tsaron Nijeriya Christopher Musa ya kai irin wannan ziyara a watan Agusta.

A tattaunawar da Yusuf Tuggar ya yi da takwaransa na Nijar Bakary Yaou Sangare, sun yi nazari kan irin ƙalubalen da ƙasashen ke fuskanta.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan barazanar ta'addanci a kan iyakokinsu, "wanda ke zama babban cikas ga aiwatar da dukkanin shirye-shiryen ci gaba mai inganci", in ji sanarwar.

Dangane da haɗin gwiwa ta ɓangaren tattalin arziki, ministocin sun tattauna kan aikin layin dogo da zai haɗa garuruwan Kano da Katsina na Nijeriya zuwa Maraɗi a Nijar, wanda ake sa ran za a ƙaddamar a 2026.

Haka kuma sun tattauna kan batun gina babbar hanyar mota wadda za ta ratsa ta cikin sahara, da kuma aikin gina bututun mai wanda zai ratsa ta cikin sahara.

Haka kuma ministocin sun tattauna kan batun jami’ansu na kwastam da batun karɓar haraji.

Ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali sun fice daga ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka a farkon wannan shekara, inda suka zargi ECOWAS da gazawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda. Ƙasashe uku ƙarƙashin jagorancin soja sun kafa nasu ƙawancen na ƙasashen Sahel.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us