TURKIYYA
2 minti karatu
Filin Jirgin Sama na Istanbul ya zama na farko da ya ƙaddamar da titin jirgi guda uku a Turai
'Ba a Turkiyya kawai ya zama na farko ba, har ma a fannin sufurin jiragen saman Turai, kuma gagarumin ci-gaba ne a fannin sufurin jiragen sama na duniya. Baya ga Amurka, Turkiyya ce kawai ƙasar da ta ƙaddamar da irin wannan aiki,' a cewar Ministan.
Filin Jirgin Sama na Istanbul ya zama na farko da ya ƙaddamar da titin jirgi guda uku a Turai
Прв во Европа: Аеродромот „Истанбул“ почнува истовремено да користи три посебни писти / AA
17 Afrilu 2025

Filin jirgin sama na Istanbul na Turkiyya, wanda shi ne na biyu mafi yawan hada-hada a Turai a bara, ya ƙaddamar da amfani da titunan jirgi uku a cikinsa.

Wannan aiki ya sa Istanbul ta zama ta farko a Turai da take da titunan jirgi har uku, sannan ta biyu a duniya bayan Amurka.

Da yake magana a wajen ƙaddamar da titin a filin jirgin sama na Istanbul, Ministan Sufuri na Turkiyya Abdulkadir Uraloglu ya ce ya zuwa ranar Alhamis, jirage uku za su iya tashi ko sauka a lokaci guda a kan titunan daban-daban waɗanda tuni aka kammala su.

'Ba a Turkiyya kawai ya zama na farko ba, har ma a fannin sufurin jiragen saman Turai, kuma gagarumin ci-gaba ne a fannin sufurin jiragen sama na duniya. Baya ga Amurka, Turkiyya ce kawai ƙasar da ta ƙaddamar da irin wannan aiki,' a cewar Ministan.

Uraloglu ya nuna cewa filin jirgin saman Istanbul Airport, wani shiri na ci-gaba na Turkiyya, ya zama wani gagarumin abu da za a nuna shi ga duniya tun bayan buɗe shi ranar 29 ga Oktoban 2018.

“Tare da yawan fasinjojin da ke sauka a cikinsa da suka kai miliyan 90 duk shekara, filin jirgin saman Istanbul ya kai Turkiyya gaba-gaba a fannin sufurin sama a duniya.

“Wannan sabon ginin na zamani, wanda ke marabtar miliyoyin fasinjoji, ya sanar da tattalin arziki da ƙarfin tsarin al’adun Turkiyya ga duniya tare da taimakawa wajen zama babbar mai ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama a duniya.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us