WASANNI
2 minti karatu
Kotu ta ɗora alhakin mutuwar ɗan wasa kan Nasarawa United da NFF
Mutuwar ɗan wasan Nasarawa United mai suna Chineme Martins, wanda ya yanke jiki yayin wasan gasar ƙungiyoyin Nijeriya, sakacin kulob ne da hukumar ƙwallo ta Nijeriya, in ji kotun ƙasar.
Kotu ta ɗora alhakin mutuwar ɗan wasa kan Nasarawa United da NFF
FIFPRO ta ce ta taimaka wa iyalan ɗan wasan wajen neman haƙƙin cewa akwai sakaci a mutuwar ɗan wasan. / Others
18 Afrilu 2025

Kotun ƙwadago ta Nijeriya ta samu Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF da laifin ‘rashin kula da aiki’ kan mutuwar wani ɗan wasa ɗan Nijeriya, shekaru biyar da suka wuce.

Shari’a kan mutuwar ɗan wasan mai suna Chineme Martins ta kammala, inda kuma aka samu ƙungiyarsa ta Nasarawa united da gazawa a lamarin mutuwar tasa.

Martins mai shekaru 25 ya yanke jiki ya faɗi sannan ya rasu yayin wani wasa da yake bugawa ƙungiyarsa ta Nasarawa United, a gasar ƙungiyoyi ta Nijeriya a Maris ɗin 2020.

Wata sanarwa ta Hukumar ‘Yan Wasan Ƙwallo ta Duniya, FIFPRO da aka fitar ranar Alhamis, ta bayyane cewa kotun Nijeriya ta samu kwamishinan wasa da laifin sakaci a mutuwar Martins.

Sanarwar FIFPRO ta ce, “Kotun ta ce hukumar gasa, da hukumar ƙwallo ta NFF, da kwamishinar wasa na ranar suna da alhakin karewa da tabbatar da ƙungiyoyi sun yi biyayya ga dokokin da aka saɓawa”.

Ƙungiyar Nasarawa United da hukumar NFF ba su yi jawabi kan wannan lamari na shari’a ba.

‘Abin ƙyama’

Hukuncin kotun, a cewar FIFPRO, ya bayyana lamarin a matsayin “abin ƙyama”, tana mai takaicin yadda aka bar Martins ya buga wasa ba tare da an masa cikakkun gwaje-gwajen lafiya ba, sannan ba tare da tanadar kayan kula da lafiya ba a filin wasa na Lafia Township Stadium.

FIFPRO ta ce, “Kotun Ƙwadago ta Nijeriya ta yi hukuncin cewa Nasarawa United ta gaza a aikinta na kulawa dangane da Martins, kuma dole kulob ɗin ya buya diyya ga iyalansa”.

Wani ɗan-uwan Martins mai suna Michael ya faɗa wa FIFPRO cewa, “Kotun ta faɗi hukuncinta kuma ta hukunta cewa Nasarawa United, da kamfanin gasa, da hukumar NFF ba su kula da kariyar ɗan-uwana ba, da lafiya da walwalarsa, wanda ya taimaka wajen mutuwarsa”.

“Ina fatan cewa za a tanadi kayayyakin kula da lafiya domin ‘yan wasan Nijeriya nan gaba, saboda kaucewa saka jimami a zukatan ‘yan-uwansu.”

Wani rahoto da aka wallafa a shafin NFF a shekarar can, ya bayyana cewa Nasarawa United ba ta da likita ko jami’in lafiyar gaɓɓai a lokacin wasan, sannan babu motar asibiti mai aiki a filin wasan yayin faruwar lamarin.

Haka nan, rahoton ya ce ba a yi wa Martins gwajin hoton zuciya a farkon duka kakar wasa uku da ya yi a ƙungiyar ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us