NIJERIYA
2 minti karatu
Ƙungiyar Miyetti Allah ta buƙaci Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin kare makiyaya a Nijeriya
Sakatare-Janar na ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Bello Gotomo ne ya buƙaci hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Ƙungiyar Miyetti Allah ta buƙaci Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin kare makiyaya a Nijeriya
Makiyaya / Getty Images
18 Afrilu 2025

Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Nijeriya (MACBAN) ta buƙaci Shugaban Ƙasa ya ba da umarni ga hukumomin tsaro don tabbatar da bai wa al’ummomin makiyaya ingantaccen tsaro a faɗin ƙasar.

Sakatare-Janar na ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Bello Gotomo ne ya buƙaci hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya kuma nemi Gwamnatin Tarayya da ta kawo ƙarshen dukkan wasu nau’ukan zarge-zargen nuna wariya da ake yi wa makiyaya a ƙasar.

Gotomo ya jaddada cewa akwai buƙatar ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro ya aiwatar da ƙwararan matakai don magance zargin ƙabilanci da nuna wariya da ƙyama da ɗora wa makiyaya duk wani laifi.

“Dole ne gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da adalci da bai wa dukkan ‘yan ƙasa kariya ba tare da la’akari da ƙabilarsu ba.”

MACBAN tana son Shugaba Bola Tinubu ya “bai wa dukkan hukumomin tsaro na ƙasar umarnin samar da ingantacciyar kariya ga al’ummomin makiyaya a faɗin ƙasar tare da kawo ƙrshen nuna wariya.”

Gotomo ya koka kan yadda ake tsare da wasu makiyaya ba bisa ka’ida ba da cin zarafinsu da kuma yadda aka tattara sunayen wasu makiyaya da zummar ƙyamatar su a kasuwar Opere da ke karamar hukumar Kabba a jihar Kogi.

“Kungiyar Miyetti Allah tana kira ga gwamnatin tarayya da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Ƙasa da kuma kasashen duniya da su gaggauta shiga tsakani,” in ji sanarwar.

Ana yawan zargin makiyaya da assasa tashe-tashen hankula da yin garkuwa da mutane da lalata gonaki a Ondo da sauran jihohin kasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us