Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka kan yakin Isra'ila da Gaza da ke gudana, yana kiran shirun da duniya ta yi game da wannan ta'addanci a matsayin “rushewar ɗabi'a,” tare da jaddada goyon bayan da Turkiyya ke bayarwa ga al’ummar Falasɗinu ba tare da gajiyawa ba.
“Kare al’amarin Falasɗinu ba kawai game da tsayawa tare da waɗanda ake zalunta ba ne,” Erdogan ya bayyana a ranar Juma’a yayin wani taro na ƙungiyoyin majalisun dokoki masu goyon bayan Falasɗinu a Istanbul a Turkiyya.
“Wannan yana nufin kare ɗan’adam da zaman lafiya, da adalci,” ya ƙara da cewa.
Tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, fiye da Falasɗinawa 51,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu.
Erdogan ya bayyana waɗannan hare-haren a matsayin “ƙazamin tashin hankali,” yana zargin gwamnatin Isra’ila da kashe fararen hula ba ji ba gani — ciki har da yara da mata da tsofaffi, har ma da jarirai.
“’Yan jarida suna mutuwa yayin da kafafen watsa labarai na duniya ke yin shiru. Yara suna mutuwa yayin da masu kare haƙƙin ɗan’adam ke kallo cikin shiru,” in ji shi.
‘Yammacin Duniya sun yi kamar ba su gani ba’
Erdogan ya soki Ƙasashen Yammacin Duniya saboda abin da ya kira rashin yin abin da ya dace cike da munafunci.
“Waɗanda suka daɗe suna alfahari da sadaukarwarsu ga ’yanci, haƙƙi, doka, da ’yancin jarida sun yi kamar ba su gani ba tsawon watanni 18 a gaban manufofin kisan kiyashi na Isra’ila,” ya ce.
Ya soki munafuncin ƙasashen da ke saurin ƙaƙaba takunkumi a wasu wurare amma suna yin shiru a wannan rikicin: “Ku, Ƙasashen Yamma, waɗanda ke amfani da makamin takunkumi ko da a kan ƙananan abubuwa, ina kuke yanzu a kan abin da ya shafi Isra’ila?”
‘Tsarin duniya da ba yake yin ko oho da waɗanda ake zalunta zai yi wa azzaluman daɗi’
“Tsarin duniya da ba ya son goyon bayan waɗanda aka zalinta zai zama wani abin la’ana da ke yi wa azzalumai daɗi,” Erdogan ya yi gargaɗi, yana nuna gazawar ƙungiyoyin duniya wajen tabbatar da ɗaukar mataki a Gaza.
Ya kuma bayyana takaicinsa game da duniyar Musulmai: “Yana da zafi in faɗi haka — kuma zuciyata tana zubar da jini — amma duniyar Musulmai ta kasa sauke nauyin da ke kanta.”
‘An kashe ‘yan jarida an salwantar da iyalansu’
Har zuwa Afrilu 2024, akalla ’yan jarida da ma’aikatan kafafen watsa labarai 212 ne aka kashe a Gaza tun farkon rikicin, wanda hakan ya sa wannan lokaci ya zama mafi muni ga ’yan jarida a tarihin zamani, a cewar Shugaban Turkiyya.
“Kwanaki kaɗan da suka gabata,” in ji Erdogan, “an kashe wata ’yar jarida tare da dukan iyalinta guda 10 — an kashe su saboda faɗin gaskiya.”
Ya nuna damuwa game da matsayin dokokin duniya: “Sun daina zama masu yi wa adalci aiki. Sun zama kayan tabbatar da ƙarfin masu ƙarfi.”
‘Yunwa a matsayin makami, gwagwarmaya tana zama ta’addanci’
Isra’ila ta taƙaita taimakon jinƙai sosai zuwa Gaza, wanda hakan ya sa Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin jinƙai suka yi gargaɗin yunwa mai zuwa.
Erdoğan ya zargi Isra’ila da amfani da yunwa a matsayin makami: “Ga waɗanda ba za su iya kashe su da bama-bamai ba, suna hana su abinci da ruwa da magani. Wannan wata manufa ce ta kisan kiyashi.”
Ya soki kiran gwagwarmayar Falasɗinu da ta’addanci: “Waɗanda suka yi shiru yayin da ake kashe Falasɗinawa yanzu suna kiran gwagwarmayar Gaza da ta’addanci — suna ƙoƙarin mayar da kisan kiyashi ya zama al’ada.”
‘Gabas ta Tsakiya na ci da wuta, duniya tana cikin haɗari’
Erdoğan ya kuma yi Allah wadai da faɗaɗa hare-haren soja na Isra’ila da suka shafi Siriya da Lebanon, yana gargaɗin cewa irin wannan ƙaruwar rikici na iya jefa yankin cikin rikici mai faɗi.
“Hare-haren da ake kaiwa Siriya da Lebanon suna nuna cewa gwamnatin Netanyahu ba ta son zaman lafiya ko kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.”
“Wannan hauka, wadda ke barazana ga yankin gaba ɗaya, dole ne a dakatar da shi nan take,” ya ce. “In ba haka ba, wannan wuta za ta cinye waɗanda ke hura ta.”
‘Za mu tsaya tare da Falasɗinu, ko da mu kaɗai ne’
Erdogan ya ƙi yarda da kowace shawara da ke nufin korar Falasɗinawa daga ƙasarsu ta tarihi: “Ko da yaushe aka gabatar da irin wannan tayin, ba shi da wata ma’ana a gare mu.”
Ya tabbatar da cewa Turkiyya ba za ta ja da baya ba: “Za mu yi duk abin da za mu iya don taimaka wa Falasɗinawa su rayu cikin ’yanci a ƙasarsu. Ko da mu kaɗai, za mu ci gaba da kare al’amarin Falasɗinu.”