WASANNI
1 minti karatu
Gola ya rasu ana tsaka da ƙwallon ƙafa a Malaysia
Firos ya rasu ne a lokacin wata gasa wadda aka shirya wa tsofaffin 'yan wasan ƙwallon ƙafa a Malaysia. Firos ya kafa tarihi a shekarun 1990s a matsayin shahararren mai tsaron raga a kungiyar Penang da kuma matakin kasa.
Gola ya rasu ana tsaka da ƙwallon ƙafa a Malaysia
An garzaya da shi asibiti nan take, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa. / others
6 Yuli 2025

Wani mai tsaron raga ya rasu bayan ya faɗi a fili yayin da ake buga wani lig ɗin ƙwallo a ƙasar Malaysia, kamar yadda kafar watsa labarai ta ƙasar ta tabbatar a ranar Lahadi.

Firos Mohamed, tsohon golan ƙungiyar Penang ta Malaysia, ya rasu bayan ya fadi yayin da ake tsakiyar wasa a gasar Dr Zambry Abd Kadir Cup wadda aka shirya wa tsofaffin ‘yan wasa.

Lamarin ya faru a filin wasa na Manjung Municipal Council Stadium a ranar Asabar da dare, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Bernama ya ruwaito.

Hukumomi sun tabbatar da cewa Firos ya rasu sakamakon bugun zuciya.

An garzaya da shi asibiti nan take, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Kungiyar Penang FC ta kuma tabbatar da wannan labari a wata sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta.

Wasu bidiyoyi da suka bazu sosai a shafukan sada zumunta sun nuna Firos, mai shekaru 53, yana faduwa yayin da yake wasa da kungiyar Kedah.

Gasar ta tattara tsofaffin 'yan wasa daga jihohi hudu — Perak, Penang, Perlis da Kedah.

Firos ya kafa tarihi a shekarun 1990s a matsayin shahararren mai tsaron raga a kungiyar Penang da kuma matakin kasa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us