NIJERIYA
2 minti karatu
NNPC ya ce wasu mutane suna shirin ɓata sunan shugabanninsa
Sanarwar da kamfanin man Nijeriya NNPC ya fitar ranar Juma'a ta ce ɓata suna ba zai hana gyaran da ake yi a kamfanin ba.
NNPC ya ce wasu mutane suna shirin ɓata sunan shugabanninsa
Kwanakin baya ne dai Bashir Ojulari ya gaji Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin man Nijeriya, NNPC / Others
27 Yuni 2025

Kamfanin man Nijeriya, NNPC, ya ce ya bankaɗo ƙulle-ƙulle da wasu mutane daga ciki da wajen kamfanin ke yi domin ɓata sunan shugabannin kamfanin.

Wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Juma’a ta ce ana yi wa NNPC zagon ƙasan ne domin yin ƙafar-ungulu game da gyaran da ake yi a kamfanin na kawar da cin hanci da rashawa da kuma ƙoƙarin mayar da NNPC kamfanin makamashi da ya dogara da ingancin aiki.

“Dabarunsu [masu zagon ƙasan] sun haɗa da ƙirƙirar labaran ƙarya na abun kunya domin kawar da hankalin shugabanni da yaudarar ‘yan ƙasar da yin zagon-ƙasa ga jajircewar ma’aikatanmu masu sadaukar da kai da kuma ‘yan Nijeriya masu son gyara,” in ji sanarwar.

“Waɗannan jerin ƙulle-ƙulle da waɗanda ke tsoron gyara da tsage gaskiya da kuma bayani game aiki ke yi— hujjoji ne ƙarara da ke nuna iirin abin da za su iya yi domin hana gyara mafi muhimmanci a cibiyar makamashin Nijeriya” in ji NNPC.

Kazalika NNPC ya ce yana tsammanin za a wallafa labaran ɓata sunan shugabanninsa nan da kwanaki da makonnin da ke zuwa.

Duk da haka, kamfanin ya ce NNPC ba zai karaya ba, yana mai cewa an fara gyara kuma babu irin zagon-ƙasan da zai iya katse gyaran.

“Muna kira ga ma’aikatanmu masu sadaukar da kai da kuma duk ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa su mayar da hankali kuma ka da su kula da surutu ko kuma su karaya,” in ji NNPC.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us