Aƙalla sojoji 17 ne suka rasa rayukansu yayin wata arangama mai zafi da ‘yan ta’adda a garin Bangi da ke Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne yayin da dakarun sojin ƙasa na Nijeriya tare da haɗin gwiwar rundunar sojin sama suka daƙile yunƙurin ‘yan ta’addan shiga garin.
A cewar sanarwar da daraktar watsa labarai ta riƙo a rundunar sojin Nijeriya Laftanal Kanal Appolonia Anele ta fitar, hare-haren sun faru ne a ranar 24 ga Yunin 2025, bayan samun sahihin bayanan sirri cewa fiye da ‘yan ta’adda 300 ne ke kokarin ketarawa ta dajin Kwanar Dutse zuwa dajin Kwatankoro.
An bayyana cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hare-hare a wasu ƙauyuka da ke makwabtaka ko kuma suna kokarin tserewa daga matsin lamba na hare-haren da sojoji ke kai musu a jihar Zamfara.
Sojojin kasa sun fafata da ‘yan ta’addan cikin daren ranar, inda aka yi artabu na tsawon sa’o’i uku. Daga bisani jiragen yakin rundunar sojin sama suka shiga kai farmaki ta sama, wanda ya tarwatsa ‘yan ta’addan da suka fara ja da baya.
Sanarwar ta bayyana cewa, "Jinin ‘yan ta’adda da dama da aka gani a hanyoyin da suka bi yayin gudu na nuna cewa sun yi babban rashi," duk da cewa ba a tantance yawan gawawwakin ‘yan ta’addan ba tukuna. Ana ci gaba da gudanar da aikin tsaftace yankin daga sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.
Sai dai sojojin sun ce abin takaici, sojoji 17 sun rasa rayukansu a fafatawar, yayin da wasu 10 suka jikkata. An kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin sojoji, kuma rahotanni na cewa suna cikin yanayi mai kyau.
Babban hafsan sojin kasa, Laftana Janar Oluwafemi Oluyede, ya nuna alhini kan rasa jaruman sojin, yana mai cewa, “sadaukarwar da suka yi don kare kasar nan ba za a taɓa mantawa da ita ba.”
Ya kuma tabbatar da cewa an ɗauki duk matakan da suka dace wajen kula da lafiyar wadanda suka jikkata.
Haka zalika, Janar Oluyede ya umarci dukkan sassan sojin da su ba iyalan mamatan cikakken goyon baya, tare da yaba jaruntaka da ƙwazonsu.
Kakakin rundunar sojin Najeriya ta ce, “Sojin Najeriya ba za su ja da baya ba wajen kare rayuka, tsaron al’umma da tabbatar da hadin kan kasa.” Ta kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanan sirri domin taimakawa yakin da ake yi da ta’addanci.