Wasu giwaye biyu suna haɗiye ƙwaya 400 ta magani kullum saboda cutar tarin-fuka
Wasu giwaye biyu suna haɗiye ƙwaya 400 ta magani kullum saboda cutar tarin-fuka
Wasu giwayen Afirka biyu Malika da Madhubala ake bai wa magungunan, waɗanda suke fama da cutar tarin-fuka, a wani tsarin kula da lafiyarsu da ake yi, wani lamari mai tsanani da ba a saba gani ba.
23 Mayu 2025

Daga Fatima Munir

Kowace safiya a gandun daji na Karachi, mai kula da dabbobi Ali Baloch mai shekaru 22 yana fara ranarsa kafin rana ta fito.

Yana dafa shinkafa da waken lentil, yana haɗa su da ɓawon rake, sannan ya cakuɗa ya murza shi zuwa ƙwallon abinci mai laushi - kowannensu cike da ƙwayoyin maganin cutar tarin fuka masu ɗaci.

Ƙwayar magani 400 cif a kowace rana.

Wasu giwayen Afirka biyu Malika da Madhubala ake bai wa magungunan, waɗanda suke fama da cutar tarin-fuka, a wani tsarin kula da lafiyarsu da ake yi, wani lamari mai tsanani da ba a saba gani ba.

Za a iya kiran wannan tsari ɗaya daga cikin manyan tsarin lula da lafiyar dabbobi mai cike da buri da aka taɓa gani a tarihin Pakistan

Ali ya ce “tabbas magungunan sun yi yawa. Amma kamar ɗan’adam, su ma suna buƙatar kulawa ta musamman. Su ma suna jin daɗi da rashinsa - kuma a yanzu mun ƙulla wata alaƙa da su.

Kula da lafiya da ba a saba gani ba

Giwayen, waɗanda ala gano suna da cutar a farkon shekarar 2025, a yanzu ana musu maganin tarin-fuka na dogon lokaci, cutar da ta yaɗu sosai a Pakistan amma kuma dabbobi ba su faye kamuwa da ita ba.

An yi gwajin cutar ne bayan da wata ƙungiyar jin daɗin dabbobi da ake kira Four Paws International ta dauki samfurin jininsu.

An gwada samfuran a wani babban asibiti mai zaman kansa a Karachi. Ana yin gwajin tarin-fuka idan aka samu kusanci da mara lafiyar da ya kamu da cutar.

Kwayoyin maganin iri ɗaya ne da wanda ake amfani da su ga ɗan’adam, kawai an daidaita su don dacewa da nauyin kilo 4,000 na kowace giwa.

Bayar da maganin tarin fuka ga giwaye abu ne mai wahala a ko yaushe," in ji Dokta Buddhika Bandara, ɗan ƙasar Sri Lanka, wanda ya tashi zuwa Karachi don jagorantar ƙoƙarin, ya shaida wa AFP.

Ya ziyarci Pakistan daga ranar 1 zuwa 17 ga Mayu kuma zai dawo wani zagaye na tantancewa bayan watanni uku.

“Amma a hankali dabbobin sun saba da tsarin.”

Shirin ya samo asali ne sakamakon babban hadin kai, karkashin jagorancin Karachi Metropolitan Corporation da kuma kwamitin fasaha mai mambobi 18 kan tarin-fuka, wanda ya hada da kwararru kan cututtuka daga Asibitin Indus da ke Karachi da manyan likitocin dabbobi da ƙwararru kan halayyar namun daji da ma'aikatan agaji.

Yayin da ba kasafai ake samun tarin fuka a cikin giwaye ba, an rubuta ta a cikin dabbobin da aka kama a Kudu da Kudu maso Gabashin Asiya. Yawanci ana kamuwa da cutar daga mutane.

"Hukumomin da abin ya shafa sun nuna matukar farin ciki wajen ba da tallafi," kamar yadda Yusra Askari, mataimakiyar sakataren kwamitin fasaha kan tarin fuka, ta shaida wa TRT World.

"Duk da rashin daidaito, mun yi nasarar tattara mafi kyawun ƙwararru - na gida da na waje - don tabbatar da Malika da Madhubala sun sami kulawar da suke buƙata."

Ƙawance mai wuyar gaske

Gwamnatin Sindh da Hukumar Kula da cutar tarin-fuka ne ke tallafawa wajen samar da maganin, tare da yin ka'idoji don kare mutanen da ke aiki a kusa da dabbobin da suka kamu da cutar.

"Bayan gano cutar, ma'aikata 11 sun yi gwajin tarin -uka - kuma duk ba sa ɗauke da cutar," Askari ya shaida wa TRT World.

"Yanzu, an ɗabbaka aiwatar da sa ido na yau da kullum da amfani da matakan kariya da matakan nesanta kansu don kare ma'aikatanmu na agaji masu ƙima."

Tawagar masu kula da giwaye su huɗu suna sanya abin rufe fuska da goge fuska yayin ciyar da giwayen don guje wa kamuwa da cutar wadda ke kama mutane fiye da 500,000 a shekara.

Wadannan ma'aikatan - musamman Ali da sauran - su ne ƙashin bayan aikin. Ba wai kawai suna ba da magani ba; suna kuma kula da dangantakar yau da kullum tare da giwayen da ke sa maganin ya yiwu.

"A farko abin yana da wuya," Ali ya tuna. "Sun ƙin karɓa. Amma yanzu abin ya zame musu jiki. Ina tsammanin sun amince da mu."

Fata bayan cire rai

Yi musu maganin dai ya biyo bayan cece-kuce da aka shafe shekaru ana yi kan walwalar giwaye a Pakistan.

Noor Jehan, wata giwa a gidan ajiye namun daji na Karachi, ta mutu a shekarar 2023 bayan koke-kone al’ummar duniya, ciki har da mawakin Amurka Cher.

Daga baya, Sonia, daya daga cikin giwaye hudu da aka kawo daga Tanzaniya a shekarar 2009, ita ma ta mutu - wani bincike da aka yi a baya ya nuna tarin-fuka ne ya kashe ta.

Yanzu haka, Malika da Madhubala su biyu ne suka rage, kuma ana sa ido sosai a kan murmurewarsu.

"Wayar da kan jama'a game da jin dadin dabbobi ya sauya sosai," in ji Askari. "Mutane a Pakistan suna daɗa sanin yadda ake bi da dabbobi - kuma suna son kasancewa cikin wannan canjin."

Hadin kan Kudancin Asiya

An tsara shirin jiyya tare da tuntuɓar masana na Sri Lanka, waɗanda suka jagoranci irin wannan rashin lafiya a yankin.

Askari ya yi imanin wannan haɗin gwiwa misali ne na haɗin gwiwar yanki a mafi kyawunsa.

"Muna matukar godiya ga Dr Rajapaksa, Dr Bandara, da abokanmu a Sri Lanka," in ji ta.

"Irin wannan hadin gwiwa wani abu ne da muke fatan ginawa a kai, saboda muna da abubuwa da yawa da za mu koya daga gare su da kuma tallafa wa juna."

Labarin da ya fi gaban na giwaye biyu kawai

Lamarin ya fi gaban ƙwaƙwar likita. Misali ne na haɗakar Lafiya da dabba da ɗan’adam, dabba, a muhalli ɗaya.

Da cututtuka irin su tarin fuka, kula da giwayen ba lamari ne na tausayi ba kawai, abu ne da ya zama wajibi.

"Wannan shari'ar ta bude ƙofa ga koyon sabbin abubuwa," in ji Askari.

"Dalibai, likitoci, da masu kiyaye muhalli suna bibiya - kowa yana kallon abin da zai yiwu idan kun sanya kulawa, daidaitawa, da kimiyya don yin aiki tare."

‘Sun san mun damu’

A dukkan wannan abin, Ali shi ne wanda ya fi kowa sanin ɗabi’un giwayen nan saboda shi ke kula da su.

“Su ma suna buƙatar a kula da su kamar ɗan’adam. Sun san mun da mu da su,”

A cikin wata goman da za a shafe ana musu magani, lallai tafiya ce mai tsawo - amma ba a bar su su kaɗai ba.


Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us