Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aika da sakonnin goyon baya a Ranar Mata ta Duniya a yayin wani buɗa-baki a watan Ramadan a birnin Istanbul, inda ya gode wa dukkanin cibiyoyin da suka hada da shirya taron musamman ma'aikatar kula da iyali da jin dadin jama'a.
Bayan mika gaisuwar Ramadan ga mahalarta taron, Erdogan ya ce: "Ina mika godiyata ga dukkan matan da suka karrama teburin buda-bakinmu inda suka halarce shi, ina rokon Allah da a Ramadan ya kawo alheri ga al'ummarmu, duniyar Musulunci da dukkan bil'adama."
Girmamawa g a ranar mata
Da yake tunatar da mahalarta taron cewa wannan rana ta zo daidai da ranar mata ta duniya, Erdogan ya bayyana cewa: A madadin kaina da matata, ina taya ɗaukacin matan kasarmu da ma duniya baki daya murnar zagayowar ranar mata ta duniya, tun daga 'yan uwanmu mata a wannan ɗakin taro, ina sake mika sakonnin hadin kai ga dukkan mata, iyaye mata, da ɗaukacin 'yan uwana mata da suke gwagwarmayar rayuwa a Falasdinu da Syria da Yemen da Libya da Somalia da Afirka da Asia da Turistan da sassa daban-daban na kasashe."
Erdogan ya bayyana cewa, cikin girmamawa yana jinjina da taya murna ga kowace jarumar mace a Gaza da suka yi jarumtaka wajen nuna adawa da zalunci da kuma yin nasara duk da kisan kiyashin da kungiyar ta Isra’ila ke yi, a madadin ɗaukacin mata a kasar.
Ya ci gaba da cewa: “Ina rokon Allah ya bai wa iyayenmu mata shahida waɗanda suka yi renon ’ya’yansu jarumai da kula waɗanda suka rasu, da kuma mata masu daraja waɗanda suke amanar shahidanmu wadanda suka waɗanda suka zubar da jininsu a kowane saƙo na ƙasarmu.
“Ba za mu ba wa jarumai mata da matan shahidan mu kunya ba daga yanzu. Za mu ci gaba da kokarin kawar da matsalar ta’addanci daga cikin al’ummarmu da kuma ci gaba da amfani da duk wata hanya da ta dace don wannan manufa”.
Ci gaba ta fannin ‘yancin mata
Erdogan ya bayyana irin ci gaban da Turkiyya ta samu a tarihi kan ‘yancin mata, yana mai cewa: “Abin lura shi ne, yayin da ‘yancin mata ba ya cikin ajanda a kasashen yamma, a hukumance mata sun fara shiga harkokin rayuwa a kasarmu tun daga shekara ta 1843.
An ba wa mata ’yancin yin hidima a shekara ta 1913. Dokar Dokar Iyali da aka samar a shekara ta 1917 wani mataki ne mai muhimmanci. Tun kafin kasashen yamma mata sun samu ‘yancin kada kuri’a kuma a zabe su a kasarmu a shekarar 1934”.
Shugaban ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da ‘yancin mata cikin shekaru ashirin da suka gabata. Ya bayyana yadda suka kafa kotunan iyali a shekara ta 2003, da kawo karshen wariyar jinsi a alakar ma'aikata, da kuma karfafa kariyar tsarin mulki don daidaiton jinsi.
Erdogan ya kara bayani dalla-dalla yadda aka samar da wuraren tsugunar da mata na tilas a manyan gundumomi, da aiwatar da shirin ƙasa na yaki da tashe-tashen hankula a cikin gida, da ɓullo da sabbin hakkoki na iyaye mata dangane da haihuwa, kiwon lafiya, da fa'idojin ritaya.
Erdogan ya kuma bayyana muhimman sauye-sauye a zamantakewar al'umma, da suka hada da cire haramcin sanya ɗankwali don tabbatar da 'yancin mata a fagen ayyukan yi da siyasa, tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar da ya tabbatar da kyakykyawan wariya bisa ka'idojin daidaito, da samar da cikakkiyar doka kan kariyar iyali daga cin zarafin mata.
Wadannan matakan, in ji shi, suna wakiltar tsarin da aka tsara don inganta kariyar doka da damar mata a cikin al'ummar Turkiyya.