Dakarun Juyin Juya Hali na Iran (IRGC) sun ce suna amfani da sabbin hanyoyi wajen kutse kan garkuwar makamai masu linzami na Isra’ila inda suke kai wa junansu hari.
A ranar Litinin IRGC sun bayyana cewa ƙarfafan bayanan sirri da ikon kayan aiki “ta hanya mai karfi da rikitarwa sama da yadda ake gani a baya” wajen hana garkuwar makamai masu linzami na Isra’ila aiki yadda ya kamata.
“An yi kutse kan garkuwar makamai masu linzami da ke da matakai da yawa, ta hanyar da garkuwar suka dinga kai wa juna hari,” in ji dakarun.
Dakarun na IRGC sun kuma ce wannan sabuwar dabara ta bayar da dama ga makamai masu linzami na Iaran wajen samun inda suka nufa “duk da babban goyon bayan Amurka da Yammacin duniya” ga fasahar kariya daga makamai masu linzami ta Isra’ila.
Iran ta bayyana wannan da cika alkawarukan da kwamandojin da aka kashe suka yi na cewa “lissafi da auna yanayin Iran da makiya masu rajin kafa kasar Isra’ila da Amurkawa na bisa kuskure.”
IRGC sun kuma yi gargaɗin cewa za a ci gaba da kai hare-hare cikin nasara kan cibiyoyin ‘gwamnati na jabu’ domin ruguza ta baki ɗaya.
Hare-Haren ranar Litinin sun kashe da jikkata gomman ‘yan Isra’ila, abin da ya ƙara ta’azzara rikicin da aka fara bayan Tel Aviv ta kai hare-hare Iran a daren Juma’a a Iran, inda ta nufi cibiyarta ta Nukiliya da ma’ajiyar makamai masu linzami, da ma kashe manyan kwamandojin soji da masanan kimiyyarta.