Kabarin Najashi: Hukumar Turkiyya ta TIKA ta gyara Masallacin Habasha mai tarihi da yaƙi ya lalata
Kabarin Najashi: Hukumar Turkiyya ta TIKA ta gyara Masallacin Habasha mai tarihi da yaƙi ya lalata
Ana kallon Kabari da Masallacin Najashi a matsayin masauki na farko ga Musulmi da suka yi hijira a Afrika.
9 Yuli 2025

Hukumar Haɗin Kai da Gudanarwa ta Turkiyya (TIKA) ta yi nasarar kammala yin kwaskwarima da kuma gyara Kabari da Masallacin Najashi a ƙauyen Najash, wanda aka sani a matsayin mazaunin farko na Musulmi a Afrika, wanda yake yankin Tigray na Habasha.

Aikin, wanda aka aiwatar tare da haɗin guiwar  mahukuntan Habasha, ya bayar da damar farfaɗo da wannan muhimmin ginin, wanda yaƙin basasa ya yi wa lahani.

Kabari da Masallacin Najashi, wanda yake Najash, waje ne da ke da dinbin tarihi da kuma muhimmanci a al'adance.

Wanda aka gina a wajejen ƙarni na 615 CE, an yi imani yana ɗaya daga cikin masallatai mafi tsufa a Afrika kuma wata sheda ce ta farko farkon Musulunci.

"A cikin ayyukan sabuntawa da gyare gyare da hukumar TIKA ta ƙaddamar, an gyara hasumiya, da manara da katanga tare da sassan katako na babban zauren masallacin," TIKA ta bayyana a wata sanarwa.

Muhimmancinsa a tarihin addinin Musulunci

"Bugu da ƙari, an kawar da duk wani tarkace kwatakwata wanda daɗewa da yanayi suka haifar da shi a illahirin masallacin," ta ƙara faɗa.

Aikin kwaskwarimar, wanda aka gudanar tare da haɗin guiwar Hukumar Adana Kayayyakin Al'adu da Tarihi da Yawon Shakatawa  ta Habasha, ta taimaka wajen maido da wajen tarihin kamar yadda ya ke a baya.

‘‘Muna godiya kan wannan aiki da aka aiwatar tare da taimakon TIKA, da Kabari tare da Masallacin Najashi, ɗaya daga cikin tarihinmu mai kima da al'adunmu a ƙetare, aka ba su kariya tare da adana su ga masu zuwa nan gaba,"

An saka wa Masallacin sunan Sarkin Najashi, adalin shugaba, wanda ya bai wa sahabban Annabi  Muhammadu mafaka lokacin hijirar farko a Musulunci.

Kabari da Masallacin Najashi, wanda ake yi wa kallon masaukin farko ga Musulmi masu hijira, an ɗauke shi a matsayin wata alama ta saukar baƙin sarkin Abisiniyawa, Najashi Ashame.

 Yiwuwar hallara don yawon shaƙatawa

 Ginin masallacin ya ƙunshi kabari bayan babban ginin, wanda ke ɗauke da kushewowi 15 na Sahabban Annabi na farko da suka yi hijira zuwa Habasha.

Hukumar TIKA ta bayyana aikin gyaran a matsayin ɗaya daga cikin "ayyukanta masu daraja".

Ginin,  wanda aka kammala aikin gyaransa a 2019, an lalata shi ne a yaƙin basasa tsakanin 2020-2022.

Tsarin masallacin yana da gaurayen zubin gargajiya da na zamanin Usmaniyya.

Kabari da Masallacin na Najashi yana da muhimmanci matuƙa ga Musulmi da ma waɗanda ba Musulmi ba.

Wata alama ce ta zaman tare da goyon baya da ke nuni da farko farkon Musulunci, sannan kuma yana nuna ɗinbin gadaddun al'adun al'ummar Habasha da ma Afrika gabaɗaya.

Ginin wani ɓangare ne na rayayyen tarihin Musulunci, da ke nuni da imani, mafaka da jajircewa.

Kabari da Masallacin Najashi yana bayar da gudunmawa wajen bunƙasa harkar yawon shakatawa a wajen kuma wata manuniya ce game da muhimmanci adana gadaddun al'adu.

A matsayinsa na alamar ɗinbin tarihi da mabanbantan al'adun Habasha, kabari da Masallacin Najashi na ci gaba da zaburarwa da ilimantar da masu kawo ziyara daga faɗin duniya.

Muhimmancinsa ya zarci muhimmancinsa na tarihi, yana nuni da wani gadadgen abin koyi da ya zarci iyakoki da al'adu.

"Da ta raya wani muhimmin gadajjen tarihi Musulunci a Afrika, Hukumar TIKA ta ƙarfafa abota kuma ta ta bayar da gudunmawa wajen farfaɗo da kyawawan al'adunmu," Hukumar Haɗin Kai da Gudanarwa ta Turkiyya ta bayyana."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us