NIJERIYA
3 minti karatu
An kashe fiye da mutane 20 a sababbin hare-hare a jihar Plateau
An kashe fiye da mutane 20 a hare-hare a jihar Flitao da ke a arewa maso tsakiyar Najeriya a wannan mako, kamar yadda jam'ian ƙarama hukumar Mangu da majiyoyin agaji suka bayyana a ranar Laraba.
An kashe fiye da mutane 20 a sababbin hare-hare a jihar Plateau
Herder-farmer attacks in Nigeria have increased in recent times as pastureland shrinks due to climate change effects. / User Upload
11 Yuni 2025

Hare-hare a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 20 a wannan makon, kamar yadda hukumomin yanki da majiyoyin agaji suka bayyana a ranar Laraba.

Hare-haren uku da aka kai a ƙaramar hukumar Mangu sun biyo bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya da aka fara tun lokacin da mutane ke haƙar ma’adanai a yankin da ke da arzikin tin, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

An jima ana samun rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato, kan samun damar amfani da filaye da albarkatun ƙasa.

Hare-hare a yankin galibi suna da alaƙa da ƙabilanci da addini, waɗanda ke haifar da ramuwar gayya tsakanin ɓangarori daban-daban.

Ramuwar Gayya

“A wani lokaci a baya, mutanen yankin suna haƙar ma’adanai, sai aka kai musu hari” da adduna, duk da cewa babu wanda ya mutu a lokacin, in ji Bala ga AFP.

Bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya, an samu hare-hare guda uku a ranar Litinin da Talata, wanɗanda suka yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 20, in ji Bala.

A daren Talata, mutane takwas sun mutu a ƙauyen Chinchin sakamakon wani hari da ake zargin Fulani ne suka kai, in ji Bala.

Wannan harin ya biyo bayan wani hari da aka kai a wajen garin Langai a ranar Litinin, inda mutane biyar suka mutu.

Makiyaya Fulani a yankin suma sun fuskanci hare-hare da cin zarafi a kwanakin baya, bayan hare-haren da ake zargin wasu daga cikin kabilar su ne suka kai, in ji Bala.

Mummunar gwagwarmaya kan filaye

Haka kuma a ranar Litinin, wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kashe mutane bakwai a yankin Bwe.

Wani jami’in Red Cross ya tabbatar da adadin mutanen da suka mutu a Chinchin kuma ya ce yawan waɗanda suka mutu a cikin sa’o’i 24 zai iya kaiwa 21.

Filayen da manoma da makiyaya ke amfani da su a tsakiyar Najeriya suna fuskantar ƙalubale daga sauyin yanayi da ƙaruwar yawan jama’a, wanɗanda ke haifar da gasa mai tsanani kan taƙaitattun filayen.

Harin ramuwar Gayya

Ƙwace filaye, da rikice-rikicen siyasa da tattalin arziki tsakanin mazauna yankin da waɗanda ake ɗauka a matsayin baƙi, da kuma ƙaruwar masu wa’azin addinai masu tsattsauran ra’ayi, sun ƙara raba kan jama’a a cikin ‘yan shekarun nan.

Idan tashin hankali ya ɓarke, rashin karfin ‘yan sanda na iya haifar da ramuwar gayya, wanda galibi ke faruwa tsakanin al’ummomi daban-daban.

A watan Afrilu kaɗai, hare-hare da aka kai a Filato da jihar Benue da ke maƙwabtaka sun yi sanadin mutuwar fiye da mutane 150.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us