Babu bilicin, babu nadama: Adawar da matan Somalia ke yi da sauya launin fata
Babu bilicin, babu nadama: Adawar da matan Somalia ke yi da sauya launin fata
Tsawon gwamman shekaru ana sayar da kayan shafe shafe masu ƙara hasken fata a shaguna da kasuwannin Somalia amma yanzu wasu ƴan Somalia suna kira da a dinga barin fata yadda Allah ya halicce ta saboda illolin da ƙara wa fata haske ke jawowa.
17 Yuli 2025

 "Shashashar mace da dare sune kaɗai baƙaƙe." Gaurayen daɗaɗɗen karin maganar Somalia irin wannan da kuma saƙonnin zamani kan kyau a dandalin sada zumunta suna haifar da abin da likitocin fata a garin ke cewa mummunar ƙaruwar matan da ke amfani da mayukan ƙara hasken fata masu haɗari domin su ƙara wa fatarsu haske.

Akwai dubban ƴan Somalia masu jan hankali a kafofin sada zumunta game da kyau da ke Somalia da ƙetare, wasunsu  na tallata fata mai dau da yin bilicin, har da kayan shafe shafen da ake iƙirarin suna mayar da baƙar fata fara.

 Ana sayar da mayukan bilicin a shaguna da kasuwannin a faɗin ƙasar tsawon gwamman shekaru, amma masana na cewa sayar da mayukan a dandalin sada zumunta da masu jawo hankalin a kafofin sada zumunta ke yi yana ƙara musu farin jini a wajen matasan mata, har ma da ƙwailaye.

Wani bincike na shekarar 2022 game da mata a babban birnin Mogadishu ya gano cewa kashi 75.6 na waɗanda aka yi hira da su sun yi amfani da man bilicin, abin da ya ce "ya ɗara ma'aunin yanki da na duniya".

Wasu masu jan hankali a kafofin sada zumuntan suna sarrafawa da kuma sayar da mayukan.

Duk da ba su da ƙwarewa a ilimin harhaɗa sinadarai, da ilimin kula da lafiyar fata ko kyau, suna kwaɓa sinadaran bilicin daban daban da sauran sinadarai su mayar da su mayukan bilicin, suna iƙirarin za su yi tasiri na ban mamaki.

Suna turo hotunansu suna da haske sosai, laɓɓansu sun yi jajawur. Waɗanda suka fi fice suna da mabiya sama da miliyan ɗaya, yayin da galibin abubuwan da suke turawa ke samun dubun dubatar yabo.

Wasu masu jan hankali a kafofin sada zumuntan kan saka lambobin wayarsu a shafukansu na dandalin sada zumunta domin mutane su iya tuntuɓar su don su sayi mayukan.

Wasu masu jan hankali a kafofin sada zumunta kan yi yunƙurin sauya ra'ayin mabiyansu kan cewa fata mai haske ta fi fata mai duhu, wani lokaci su yi amfani da hotuna da bidiyo da aka jirkita.

Abin da ya sa bilicin ya zama wata ɓoyayyiyar 'annoba'

"Ina sarrafa mayukan fuska iri uku daban daban yayin da kowanne daga cikinsu ke yin aikinsa daban," ɗaya daga cikin masu jan hankali a kafofin sada zumuntan ta gaya wa mabiyanta da ba su san dawar garin ba yayin wani shirin matambayi ba ya ɓata a kafar sada zumunta wanda aka kalla kusan sau 360,000.

Hotunan bidiyonta sun nuna wasu akwatina maƙare da mayukan bilicin iri iri da take sarrafawa.

Ɗaya daga cikin bidiyoyinta wanda yake nuna ta tana shafa mayuka iri iri a fuskarta mai haske sosai an kalle shi sau miliyan 1.3.

Masu jan hankali a kafofin sada zumuntan ba sa taɓa bayyana haɗarin da bilicin zai iya haifarwa.

Likitan fata Dr Muhamed Mude, wanda ya assasa cibiyar kula da kyau da lafiya ta Bidhaan Beauty and Health Centre a Mogadishu, ya ce kimanin kashi 60 na masu jinya a wurinsa suna fama da ƙaiƙayin, ja bau da kuma ciwon fata sakamakon yin amfani da mayukan, amma kaɗan daga cikinsu ne suka fahimci haɗarin da ke tattare da hakan.

"Galibin kayan shafe shafe da ke yin bilicin sun ƙunshi sinadarai masu illa kamar  hydroquinone da mercury da ke haifar da ƙaiƙayi da abubuwa marasa daɗi da kuma illa ta tsawon lokaci da ta haɗa da tsukewar fata da kuma ƙaruwar rashin son hasken rana ya taɓa ta," ya faɗa.

Ta'amali da sinadarin mercury zai iya haifar da lalacewar ƙoda, nakasu wajen ji da gani da furuci, da rashin natsuwa, karkarwa da sakewar jiki. Za ma a iya harbin jarirai da cutar ta hanyar shayarwa.

Ƙasashen Afrika da dama da suka haɗa da Afrika ta Kudu, Kenya, Ivory Coast da Ghana sun haramta sayar da kayan shafe shafe masu saka bilicin amma babu dokar haramci a Somalia.

Akwai mayukan bilicin jibge a shaguna da kasuwanni a faɗin ƙasar. Kowa zai iya sayan su ba tare da la'akari da shekarun mutum ba.

Daga mai goyon bayan bilicin zuwa mai adawa da shi

Iman Osman tana gudanar da cibiyar kula da fata ta Maariin Skincare Centre a Mogadishu inda take sayar da kayan shafe shafe.

Tana ƙoƙarin sauya wa mata ra'ayi da su dinga amfani da kayan shafe shafe na gargajiya marasa lahani a kafofin sada zumunta da kuma tattaunawa da abokan hulɗar kasuwancinta ido da ido a shagonta.

"Galibin ƴan Somalia ba su tsinkayi haɗuran da ke tattare da amfani da mayukan bilicin ba ne," ta bayyana.

"Wasu sun san suna da haɗari amma suke amfani da su, saboda sun fi son fata mai haske, kuma mayuka marasa lahani za su iya fin tsada.

"Akwai buƙatar gudanar da gagarumin gangamin wayar da kai domin faɗakar da jama'a kan haɗarin da ke tattare da kayan shafe shafe masu saka bilicin,"ta faɗa. Akwai buƙatar mata su gudanar da shi.

Wasu ƴan Somalia sun rungumi launin fata fara dau tsawon daruruwan shekaru, inda ake kallon mace mai fata mai haske ita ce ƙololuwar kyau.

“Kowa na son samun fata mai haske saboda al'ummarmu a galibin lokaci suna yi wa mutane hukunci ne bisa launin fata da suke da shi," a cewar Hoda Dahir Maxamad a birnin tsakiya na Jowhar.

Amma akwai alamun kyakkyawan fata, musamman daga waɗanda suka yanke tsammani wajen zamar da fatarsu mai haske.

"Na yi wa fatata bilicin na tsawon shekaru biyar," a cewar Warsan.*

"Na dena bayan na fara samun ƙananan tabbuka a fatata kuma ba na iya shiga rana. Yanzu ina gayawa ƴan'uwana da ƙawayena cewa lafiyayyiyar fata ta fi fata mai haske."

Ƙurajen fuska da ake kira fimfus suna ɓata wa mutum rai ta hanyoyi da dama

'Baƙi kyau ne'

Aisha ƴar jarida ƴar shekaru ashirin da bakwai da haihuwa ta fara amfani da mayukan bilicin tun tana ƙwaila.

"Fatata baƙa ce kafin na fara amfani da mayukan bilicin," ta bayyana. "Bayan shekaru uku fatata ta soma ƙin hasken rana amma na ci gaba da amfani da mayukan na tsawon sama da shekara goma."

 Har sai da aka kwantar da Aisha a asibiti kafin ta daina bilicin.

"Wata rana na faɗo daga matattakala a wajen aiki," ta bayyana. "Raunin da ke ƙafata ya ƙi ya warke. Na je asibiti har guda biyu sai likitocin suka ce fatata ba za ta ɗinku ba saboda man bilicin ya tsuke ta. Sun shawarce ni da na dena bilicin kuma na karɓi shawararsu."

"Warsun da Aisha ba su kaɗai ba ne. Wasu matan Somalia sun yanke shawarar dena ƙara wa fatarsu haske, amma ba sa so su tattauna batun a bainar jama'a.

Galibin waɗanda aka yi hira da su sun ce sun dena amfani mayukan ne bayan sun fahimci irin illar da suke yi wa fata da ma lafiya ɗungurungun.

Wasu sun ce yanzu sun san baƙi kyakkyawa ne kuma gara su alkinta fatar da suke da ita maimakon su lalata ta da zimmar zama fara.

*Warsan ba sunanta na asali ba ne. 

Marubutan, Kiin Hassan Fakat, Naima Said Salaah and Haliima Mahomad Asair, masu aiko da rahotanni ne da ke aiki da Bilan, ƙungiyar ƴanjarida mata zalla ta farko a Somalia, ƙarƙashin kafar yaɗa labarai ta Dalsan Media Group, Mogadishu.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us