NIJERIYA
2 minti karatu
Mutanen da 'yan ta'adda suka kashe a Nijeriya a wata shida a 2025 sun fi na 2024 yawa
Adadin mutanen da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga suka kashe a watanni shida na farkon shekarar 2025 ya haura na shekarar 2024 baki daya, in ji Hukumar Kare Hakkokin Dan'adam ta Nijeriya.
Mutanen da 'yan ta'adda suka kashe a Nijeriya a wata shida a 2025 sun fi na 2024 yawa
Nijeriya na fama da hare-haren 'yan bndiga da garkuwa da mutane / Others
9 Yuli 2025

Alkaluman da Hukumar Kare Hakkokin Dan’adam ta Nijeriya ta fitar sun bayyana cewa a watanni shida na farkon 2025, ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun kashe a kalla mutum 2,266 a kasar.

Wannan adadi ya zarta na watanni shidan farko na 2024 inda aka kashe mutum 1,083, sannan a shekarar gaba daya kuma suka kashe jimillar 2,194.

Sojojin Nijeriya na yaƙi da ‘yan ta’addar Boko Haram a arewa maso-gabas da ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a arewa maso-yamma, da ƙoƙarin daƙile hare-haren makiyaya a tsakiyar kasar da kuma ‘yan-a-ware a kudu maso gabashin kasar.

Lamarin ya ta’azzara a baya bayan nan, inda a watan da ya gabata kadai aka kashe mutum 606, ciki har da harin ‘yan bindiga a yankunan Yelewata da Dauda na jihar Benue inda aka kashe mutum 200.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Kare Hakkokin Dan’adam ta Kasa Tony Ojukhu, ya bayyana alkaluman a yayin wani taro a Abuja, inda ya yi kira da a dauki matakan da suka kamata daga bangaren gwamnati.

“Wadannan ba alkaluma ne na rahotanni kawai ba; ana maganar iyaye maza da mata, yara kanana, da ‘yan’uwa da dangi da aka ɗaidaita, aka lalata jin dadin rayuwarsu, sannan aka dusashe hasken makomarsu ta mummunar hanya,” in ji Ojukwu.

Hukumar ta kuma bayar da rahoton cewa an yi garkuwa da mutum 857 a watanni shida na farkon 2025, duk da cewa an samu ragi idan aka akwatanta da mutum 1,461 da aka yi garkuwar da su a watanni shidan farko na 2024.

Kazalika, rahoton ya lura da yadda ake kai hare-hare kan jami’an tsaro da ‘yan sintiri na yankuna, inda aka kashe sojoji sama 17 a jihohin Kaduna da Neja, da mambobin ‘yan bijilante fiye 40 a jihar Zamfara ta arewa maso-yamma.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us