An fara gudanar da Taron Diflomasiyya na Antalya karo na 4 a birnin hutawa na Turkiyya, inda ake tattara shugabannin duniya, jami’an diflomasiyya, masu tsara manufofin kasashe, kwararru, da malaman jami’o’i don tattauna kalubalen da duniya ke fuskanta a yau a yayin da ake samun sauye-sauye.
An fara gudanar da taron a ranar 11 ga Afrilu tare da jawabin bude taro daga Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan.
Taron da za a gudanar a cikin kwanaki uku, na da taken ‘Farfado da diflomasiyya a duniyar da ake samun rarrabuwar kawuna' da kuma manufar yadda za a sake dabbaka diflomasiyya wajen warewar rike-rikicen yankuna da duniya baki daya.
Ana sa ran taron zai samu mahalarta 4,000, ciki har da sama da shugabannin gwamnatoci 20, sama da ministoci 70 - sama da 50 daga ciki na harkokin kasashen waje - da wakilan kungiyoyin kasa da kasa su kimanin 60.
Daga cikin wadanda ke halartar taron har da malaman jami’o’i, kwararru, da dalibai. A yayin da tawagogi suka fara halarta, tuni aka fara hada-hada a Filin Jiragen Sama na Antalya.
An tantance wakilai 450 daga kasashen duniya kusan 140 da kusan ‘yan jaridu 950 daga kusan kasashe 50 a wajen taron.
Za a yi zama sama da 50 a wajen taron, za a tattauna batutuwan siyasa, daga Gabas ta tsakiya zuwa Asia-Pacific, Afirka zuwa Latin Amurka, da manyan batutuwan duniya kamr sauyin yanayi, yaki da ta’addanci, taimakon jin kai, samar da abinci, da kirkirarriyar basira.
Daga cikin manyan mutanen da za su halarci taron ar da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev, shugaban kasar Jumhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus Ersin Tatar, shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud, shugaban kasar Montenegro Jakov Milatovic, shugaban Saliyo Julius Maada Bio.
Akwai kuma Shugaban Ƙasar Indonesia Prabowo Subianto da na Guinea-Bissau Umaro Sissoco EMbalo, shugaban kasar Hungary Viktor Orban da shugaban kasar Kosovo Vjosa Osmani-Sadriu.
Zuciyar Diflomasiyya
Gwamnan Antalya Ersin Sahin ya bayyana farin cikinsa na karbar bakuncin kashi na hudu na taron a wannan shekara.
Sahin ya yi karin haske da cewa Antalya, birnin da ya yi shuhura a duniya, zai marabci shugabannin kasashe da gwamnatoci, ministocin harkokin kasashen waje, wakilan kungiyoyin kasa da kasa da dama, malaman jami’o’i da ‘yan jaridu a wajen taron. Ya bayyana nasarar da birnin ke samu wajen daukar nauyin manyan taruka na kasa da kasa.
Ya tunatar da cewa a baya Antalya ya krbi bakuncin manyan taruka irin su Taron Manyan Kasashen Duniya na G20 da NATO, Sahin ya kuma kara da cewa “Muna alfahari kan yadda diflomasiyya ke tasowa, habaka da girma a Antalya, kuma birnin na zama cibiyar warware rikice-rikicen kasa, yankuna da ma duniya baki daya ta hanyar tattaunawa.”
Ba wai iya taron Diflomasiyya za a yi a nan kawai ba, har ma da Taron Majalisun Dokoki da na Ministocin Harkokin Wajen NATO, kuma a 2016, za a gudanar da taron sama jannati mafi girma a duniya a Antalya. Birnin na alfahari da za cibiyar gudanar da manyan taruka na kasa da kasa.
Sahin ya kara da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen karbar bakunci da daukar nauyin taron. Ya ce “Mun fara marabtar baƙinmu.”
“Duk otel ɗinmu sun shirya. Antalya ba wai birnin Turkiyya kawai ba ne, birni ne na duniya baki daya.”