TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya na ta ƙoƙarin kashe gobarar daji da ke ci a wasu yankunan ƙasar
Ma’aikatan kashe gobara na aiki ba ƙaƙƙautawa, inda ake bayar da taimako ta sama da jiragen sama 27 da jirage masu saukar ungulu 105, da jirage marasa matuƙa 14.
Turkiyya na ta ƙoƙarin kashe gobarar daji da ke ci a wasu yankunan ƙasar
Ana ta kokarin kashe wutar dajin da suka kama a wasu sassan Turkiyya. / AA
1 Yuli 2025

Turkiyya na fuskantar daduwar gobarar daji sakamaon farawar lokacin zafi, inda mahukunta suka ce tun 1 ga watan Yuni an samu kamawar gobarar dajin sau 1,516.

A wata sanarwa da aka fitar ta shafin X a ranar Litinin, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tabbatar da cewa jami’an kashe gobara na aiki ba ƙaƙƙautawa, kuma suna samun taimako ta sama daga jiragen sama 27 da jirage masu saukar ungulu 105, da drone 14.

Kusan motocin kashe gobara 6,000 tare da ma’aikatan kwana-kwana 25,000 ne aka fara aikin kashe wutar da su.

“Ya zuwa yanzu, an kashe gobara 1507. Jiragen sama sun yi safara sau 10,260, inda suka zuba ruwa sama da tan 33,000 don kashe wutar,” in ji Erdogan.

Ya kuma ce an kama mutane 31 da ake zargi da cinna wutar. An tsare goma a hukumance, an kuma saki wasu goma bisa sharadin sanya musu idanu daga bangaren shari’a har zuwa a kammala bincike.

Shugaba Erdogan ya mika jajensa ga ‘yan kasar da ibtila’in gobarar ya rutsa da su inda ya yi gargadin cewar kusan dukkan dazukan kasar sun kama da wuta, wadda aka cinna da gangan ko sakacin mutane.

“Kasarmu, na daukar matakan kariya, amma ina son tuna wa kowa cewar babban riga-kafi shi ne a kaucewa cinna wutar,” in ji Erdogan, yana mai kira ga ‘yan kasa da su kula sosai a watannin da ke tafe.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us