Kalaman da kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China ya yi, inda ya ce: “Idan yaƙi Amurka ke so, ko yaƙin sanya haraji ko na kasuwanci, ko ma wane irin yaƙi ne, mun shirya mu yi shi har sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi,” ya jawo cece-kuce sosai.
Wasu sun fassara kalaman a matsayin waɗanda suka ta’azzara yaƙin cacar bakan daga ɓangaren China.
Wannan magana ta yi matukar jan hankali, domin ba kasafai ake jin irin waɗannan kalamai kai tsaye daga Ma’aikatar Harkokin Wajen China ba, balle kuma a yaɗa su a shafukan sada zumunta na hukuma a duniya.
Waɗannan ba irin kalaman da ake ji daga Ma’aikatar Tsaro ko Jaridar Global Times, ko kuma daga wasu jakadun diflomasiyyar da ake kira 'yan “matsattsaku masu bakin magana” ba, wadanda ko dai suna magana ne ba tare da izini ba ko kuma suna kwaɓo duk abin da ya fito daga bakinsu.
Wannan kalami ya fi daukar hankali musamman saboda a watannin baya kafin zaben Amurka, kalaman hukuma daga China da rahotanni daga kafafen yada labarai na gwamnatin ƙasar sun kasance masu sassauci ga Washington, suna jiran ganin wace hanya Donald Trump zai dauka ba tare da shiga cikin wani yanayi na fito-na-fito ba, kamar yadda Trump ya saba yi.
Yanzu, da yake bayyana cewa sabuwar gwamnatin Amurka tana daukar matakai masu tsauri kan China, wannan sabon kalami kai tsaye yana nuna cewa an cire sassaucin da aka fara a baya, aƙalla a fagen magana.
Hakan na iya nuna cewa Beijing na shirin shiga wani sabon mataki na yin fito-na-fito da Amurka kai tsaye.
Idan kuma Amurka ta janye daga rikicin Ukraine, ta mayar da hankali gaba ɗaya kan China, kamar yadda wasu ke hasashe, to yanzu ne lokacin da Beijing za ta tsaya tsayin daka, har ma ta nuna cewa tana shirye don yaƙi idan Amurka ta tsokano ta.
A gefe guda, wannan matsayi ya dace da ikirarin Beijing cewa a wannan sabon zamani, China ta dawo tsakiyar matakin duniya a matsayin babbar kasa, wadda ke taka rawa wajen tabbatar da duniya mai bangarori da dama.
A daya bangaren kuma, Trump ya nuna muhimmancin yin taka-tsan-tsan wajen mu’amala da Rasha, yana yawan nuna yiwuwar ɓarkewar yakin duniya na uku idan aka yi kuskure wajen tafiyar da dangantaka.
Wannan yana bayar da muhimmin yanayi yayin da Trump ke kokarin warware rikicin da Biden ya yi da Rasha: shugabannin Amurka sun yi alkawarin kayar da Rasha da kuma lalata tattalin arzikinta.
Amma ga shi yanzu, shugaban Amurka na iya tattaunawa kan sharuddan da za su tabbatar da nasarar Rasha, ba tare da hadin-kan ƙawayensa ko ma Ukraine ba.
Darasi ga Sin ya bayyana: idan Trump yana tsoron yaki mai fadi da Rasha, idan Rasha ta tsaya tsayin daka kan NATO, Ukraine, Turai da Amurka, tare da tattalin arzikinta ya tsira daga hare-haren tattalin arziki, to Sin, wadda ta fi Rasha karfi a tattalin arziki da soja, ya kamata ta tsaya tsayin daka ba tare da wata fargaba ba, musamman idan gwamnatin Trump na shirin gwada karfinta.
A bara, akwai wata fahimta a Beijing cewa wa’adi na biyu na shugabancin Trump zai fi dacewa da muradun China.
Duk da haka, akwai wadanda suka damu cewa warware rikicin Ukraine zai ba Washington damar mayar da hankali kan China. Amma za a iya cewa Amurka ta yi amfani da wannan rikici wajen lalata dangantakar China da Turai.
A halin yanzu, gwamnatin Biden ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da dabarun taƙaita China, har zuwa wani mataki da hadarin yaki ya yi matukar karuwa a 2023, wanda ya sa dole a yi sassauci.
A lokaci guda, ya kara bayyana cewa manufofin Amurka ba za su yi nasara a Ukraine ba.
Za a iya cewa shekarar 2023 ta nuna gazawar dabarun Amurka, tana nuna iyakokin karfinta wajen dawo da tsarin duniya mai bangare daya.
Wannan shekarar ta biyo bayan karuwar kwanciyar hankali a tattalin arzikin China da kuma manyan ci gaba a fasaha, wanda ya nuna rashin amfani na takunkumin fannin fasaha da Amurka ta ƙaƙaba.
Saboda haka, dabarun Biden sun gaza. Duk da cewa dawowar Trump na iya bai wa Amurka damar sauya dabaru, China ta yi imanin cewa zai kasa samun goyon bayan kasa da kasa kan China fiye da magabacinsa.
Sun yi tunanin zai ƙara rura rikice-rikice a tsakanin ƙawayen Amurka da kuma cikin Amurka kanta, tare da yiwuwar tattaunawa kan yarjejeniyar ciniki, kamar yadda ya faru a wa’adin farko na shugabancinsa.
Hakan na faruwa ne saboda yaƙin ciniki yana kawo wahala ga Amurkawa, kuma ba da daɗewa ba, abokan Trump a Majalisa za su fuskanci masu zabe da ke son zaman lafiya da rage hauhawar farashi da ya yi musu alkawari.
Hakika, idan ‘yan Republican suka rasa ikon Majalisa, dawowar Trump za ta kasance wata gazawa ta biyu, kuma za a yi masa kallon wani “shugaba marar ƙarfin iko ko marar tasiri”.
Duk da cewa Trump bai bayyana dukkan dabarunsa ba, Beijing na ganin Amurka na bincikar hanyoyi uku na dabarun siyasa a lokaci guda.
Na farko, zai iya daukar matakin raba kai da taƙaita China gaba daya. Amma wannan na iya haifar da yaƙi na tattalin arziki wanda zai iya tursasa China ta kalubalanci darajar dala.
Wannan kuma na iya kaiwa ga rikici na soja, ganin cewa tattalin arzikin Amurka (kuma karfin sojanta) ya dogara sosai kan darajar dala a matsayin kudin duniya.
Na biyu, zai iya daukar matakin janyewa daga wasu yankuna, ya koma kan manufofin New Monroe Doctrine, kamar yadda wasu matakansa ke nuna ya mayar da hankali kan yankin yammacin duniya inda Amurka ke da fifiko ta fuskar yanayi.
Wannan na iya zuwa tare da matakai kan Greenland da Kanada, ganin muhimmancin yankin arewa ta fuskar sauyin yanayi.
A halin yanzu, China da Rasha za su fuskanci kalubale wajen tsara matsayinsu a tsakiyar Asiya, duk da ci gaban da suka samu ta hanyar hadin gwiwa a karkashin Belt-Road Initiative da BRICS, da kuma Shanghai Cooperation Organisation.
Na uku, Trump na iya tattara ƙarfi don cim ma wata babbar yarjejeniya, inda yake fatan samun kariya daga China kan darajar dala da tattalin arzikin Amurka, da muradun siyasa a yankin Amurka, tare da karfafa zuba jari da masana’antu daga Sin zuwa Amurka, da kuma samun fifiko kan Turai.
Wannan yiwuwar tana jan hankalin Beijing kuma tana firgita Turai, kuma daga cikin hanyoyin uku, ita ce mafi yiwuwa, wadda za a iya cim ma kafin Majalisar ta kai ga zaben tsakiyar wa’adi.
Ya dace a ce Sin ta fahimci wadannan dabaru da hanyoyin siyasa masu yiwuwa, kuma tana da shirye-shiryen gaggawa don tunkarar kowanne.
A halin yanzu, nuna damuwa ko firgici ba abu ne da Beijing ke son bayyanawa ba, domin wannan shi ne abin da Trump ke kokarin jawowa.
Abu na karshe da yake so ya ji shi ne cewa wata kasa da ta fi Rasha ƙarfi tana shirye don yaƙi. Kuma ba kamar Kanada da Mexico da Panama, da Colombia ba, Sin ba za ta bari a takura mata ta yi sassauci ba.