Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana wa takwarorinsa na ƙasashen Musulmi cewa Isra'ila tana jefa yankin cikin "babban bala'i" ta hanyar hare-harenta kan Iran, kuma ya ƙara da cewa manyan ƙasashen duniya dole ne su hana yaƙin rikiɗewa zuwa rikici mai girma.
Da yake jawabi a taron ministocin harkokin wajen Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da aka gudanar a Istanbul, Fidan ya yi kira ga ƙasashen Musulmi su goyi bayan Iran kan Isra'ila, yana mai cewa yankin yana da "matsala da Isra'ila" bayan yaƙin kisan kiyashi da ta yi a Gaza da hare-harenta kan Lebanon, Syria, Yemen da Iran.
“Isra'ila ta aikata kisan ƙare-dangi kuma ta jawo zubar da jini a Gaza, kuma abin takaici, Isra'ila a yau tana kai hari kan Iran, tana jefa dukkan yankin cikin bala'i,” in ji Fidan a lokacin da yake gargaɗi.
Taron ya gudana ne a yayin da ake fama da ƙarin tashin hankali, inda hare-haren Isra'ila suka kai ga Iran, Lebanon da kuma kisan ƙare-dangi da Tel Aviv ke yi a Gaza.
‘Matsalar Isra'ila’
Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila, yana mai bayyana su a matsayin tushen rashin zaman lafiya a yankin, yana mai ƙara jaddada cewa ba kawai matsala ce ta Falasɗinu, Iran, ko Syria ba.
“Wannan ba matsalar Yemen, Iran, Falasdinu, ko Syria ba ce. Matsalar gaske ita ce Isra'ila,” in ji Fidan, inda ya yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren Isra'ila a yankin.
Ya kara da cewa Turkiyya tana shirin ta tallafa wa ƙoƙarin diflomasiyya don rage tashin hankali ƙarƙashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
Fidan ya kuma jaddada buƙatar ƙasashe mambobin OIC su yi aiki tare cikin hadin kai kuma su nuna cikakken goyon baya ga Iran kan tayar da hankali da Isra'ila ke yi.
“Ƙasashen mambobin Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmi su yi aiki tare cikin hadin kai, kuma muna da yaƙinin cewa ƙasashen mambobin OIC za su nuna cikakken goyon baya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” in ji shi.