NIJERIYA
1 minti karatu
Mutum 20 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Neja
Lamarin ya faru ne a al’ummomin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na ƙaramar hukumar Mokwa, sakamakon mamakon ruwan da aka yi a ranar Laraba da daddare.
Mutum 20 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Neja
Ambaliya a Nijeriya / Others
29 Mayu 2025

Aƙalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta faru a jihar Neja, kamar yadda jaridun Nijeriya suka rawaito.

Lamarin ya faru ne a al’ummomin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na ƙaramar hukumar Mokwa, sakamakon mamakon ruwan da aka yi a ranar Laraba da daddare.

Kazalika rahotanni sun ce an ceto mutum uku daga cikin 33 da ruwan ya tafi da su, kuma har yanzu ba a ga mutum 10 ba.

Ruwan da aka zabga ya rushe gidaje kusan 50 a yankunan tare da lalata manyan hanyoyin yankunan da dama.

Da yake tabbatar da lamarin, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta NEMA, Abdullahi Baba Arah ya ce hukumar ta karɓi rahoton mummunar ambaliyar ruwan da ta lalata al’ummomin biyu.

Arah ya kuma tabbatar da mutuwar mutanen, yana mai cewa ana ci gaba da aikin ceto.

Wannan ita ce ambaliya ta farko da aka samu a daminar bana.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us