SIYASA
3 minti karatu
A shirye Turkiyya take ta taimaka wajen kwantar da rikicin Isra’ila da Iran: Erdogan
Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da shugaba Pezeshkian na Iran, da Putin na Rasha, inda suka taɓo batun rikicin Isra’ila da Iran da sauran batutuwan yankunansu.
A shirye Turkiyya take ta taimaka wajen kwantar da rikicin Isra’ila da Iran: Erdogan
Erdogan ya jaddada cewa Turkiyya na sanya idanu da bin diddigin rikicin na Isra'ila a Iran. / Anadolu Agency
16 Yuni 2025

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ƙara yunƙurin diflomasiyya don kwantar da rikicin Isra’ila da Iran, inda ya yi tattaunawa ta wayar tarho a ranar Litinin da Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin.

Shugaba Erdogan ya jaddada shirin Turkiyya na taimakawa wajen kwantar da rikicin, inda ya yi gargaɗi game da hatsarin yaɗuwar yaƙi a yankin, ya kuma buƙaci dukkan ɓangarori da su dawo teburin tattaunawa da diflomasiyya.

A tattaunawarsa ta wayar tarho da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian, shugaba Erdogan ya taɓo batun taɓarɓarewar rikici tsakanin Isra’ila da Iran. Erdogan ya ce a shirye Turkiyya take ta taka rawa don tamakawa wajen kwantar da rikicin, tare da dawowa kan tattaunawar nukiliya, kamar yadda Sashen Sadarwa na Turkiyya ya sanar.

Shugaban na Turkiyya ya kuma ce yana ta tattaunawa da shugabanni a yayin da rikicin ke ci gaba. Erdogan ya kuma kara jaddada muhimmancin da Ankara ke bai wa zaman lafiya a yankin.

Tattaunawa ta wayar tarho da Putin

Erdogan ya kuma tattauna ta waya da shugaba Putin, inda a nan ma suka taɓo batun kwantar da rikicin Isra’ila da Iran, da ma batutuwan yankin.

Shugaban ƙasar na Turkiyya ya kuma yi gargaɗin cewa rikicin da Isra’ila ta janyo ta hanyar kai wa Iran hari na barazana ga tsaron dukkan yankin. Ya kuma soki yadda Isra’ila ke take dokokin ƙasa-da-ƙasa wanda ya bayyana a matsayin barazana ƙarara ga tsarin duniya.

Erdogan ya jaddada buƙatar aiki da diflomasiyya, yana mai cewa yankin ba zai sake jurewa wani yaƙin ba.

Da yake bayyana ayyukan diflomasiyyar Turkiyya, shugaban na Turkiyya ya ce warware rikici da Iran na buƙatar tattaunawa da sulhu, inda ya buƙaci dukkan ɓangarori da su koma teburin sulhu.

Erdogan ya kuma yi gargaɗi kan hare-haren baya-bayan nan za su iya janye hankulan mutane daga rikicin jin-ƙai a Gaza, inda ya yi gargaɗin cewar Isra’ila na iya janyo mummunan yanayin da ba za a iya sauya shi ba.

Shugaba Putin ma ya nuna goyon baya ga damuwar ta Erdogan, yana mai bayyana yardarsa kan dole ne a samar da tsagaita wuta nan da nan, tare da bayar da dama ga ƙofar diflomasiyya.

Ƙaruwar tashin hankali a yankin

Tun ranar Juma’a rikici ya ɓarke a yankin, bayan Isra’ila ta kai hare-hare ta sama kan wurare daban-daban a Iran, ciki har da cibiyar nukiliya, wanda ya sanya Tehran ɗaukar matakin ramuwa.

Mahukuntan Isra’ila sun ce aƙalla mutane 24 aka kashe tare da jikkata wasu ɗaruruwa a hare-haren da Iran ta kai da makamai masu linzami cikin ƙasar, tun ranar Juma’a.

A nata ɓangaren, Iran ta ce an kashe mata mutane 224 tare da jikkata sama da 1,000 sakamakon hare-haren na Isra’ila.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us