NIJERIYA
4 minti karatu
Ambaliya: Jihohin Nijeriya 20 na cikin hatsari duk da ware tallafin Naira biliyan 620
Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta fitar da gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a watan Yuli a jihohin Sakkwato, Lagos, Edo, Benue da wasu karin jihohi 16.
Ambaliya: Jihohin Nijeriya 20 na cikin hatsari duk da ware tallafin Naira biliyan 620
Ana yawan samun ambaliyar ruwa a jihohin Nijeriya musamman a watannin Yuli da Agusta da aka fi samun ruwan sama. / AP
8 Yuli 2025

Rahoton Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) da aka fitar a ranar Litinin ya bayyana jihohin da ka iya fuskantar ambaliyar ruwa a watan Yuli.

Hukumar ta ce Jihar Sakkwato ce ta fi fuskantar tsarin yiwuwar samun ambaliyar ruwa.

Rahoton na NiMet ya ce “Jihar Sakkwato na fuskantar babban hatsarin samun ambaliyar ruwa.

Sauran jihohin da su ma suke fuskantar irin wannan hatsari sun haɗa da Kaduna, Zamfara, Yobe, bauchi, Bayelsa, Jigawa, Adamawa, Taraba, Neja, Nassarawa, Ogun, Ondo, Delta, Edo, Cross River, Rivers da Akwa Ibom.”

Shawarwari ga mazauna jihohin

Hukumar ta bai wa jama’ar wadannan jihohi da ka iya fuskantar ambaliyar ruwa a watan Yuli wasu shawarwari don kare su daga ɓarnar ambaliyar.

Shawarwarin da aka bayar sun haɗa da sauya matsugunai idan hakan ya zama dole, share magudanan ruwa, shirya kayan agajin gaggawa, kashe lantarki da iskar gas a lokutan ambaliya, karfafa matakan magance zaftarewar ƙasa da yawaita wayar da kan jama’a.

Sama da gidaje 500 sun lalace a jihohin Kogi da Kebbi

Wannan gargadi daga Hukumar Kula da Yanayin ta Nijeriya na zuwa ne a yayin da a makon da ya gabata aka samu ambaliyar ruwa mummuna a jihar Ondo da ke kudu maso-yammacin Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewar ambaliyar ruwan ta yi ɓarna a yankunan Uso, Ayeka, Ikoya, Igbodigo, Igodan, da Igbotako na jihar inda jama’a suka nemi gwamnati da ta kai musu agaji.

A jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya ma ambaliyar ruwan ta yi mummunar barna inda aka samu asarar dukiya da dabbobi.

A yankin Kabba, sama da gidaje 500 ne ruwa ya mamaye bayan mamakon ruwan saman da aka samu na tsawon kwanaki uku.

Wani jami’in Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kogi ya bayyana cewa sun samu labarin ibtila’in, amma suna ci gaba da tattara rahotanni a kai.

A jihar Kebbi da ke arewa maso-yammacin Nijeriya, an samu ambaliyar ruwan da ta illata aƙalla gidaje 60 a garin Zogirma na yankin ƙaramar hukumar Bunza.

Mazauna yankin sun shaida cewa an samu guguwa tare da ambaliyar ruwa, inda aka yi asarar dabbobi da kadarori na miliyoyin Naira, mahukuntan yankin sun yi alkawarin tallafa wa wadanda ibtila’in ya rutsa da su.

An zargi jihohi da ɓarnatar da kuɗaɗen magance kwararowar hamada

An shiga wannan yanayi ne a lokacin da wasu Kungiyar Kula da Lafiyar Muhalli da ke bincike kan sabawa da sauyin yanayi da Cibiyar Masu Tsara Birane ta Nijeriya da wasun su ke suka gwamnatocin jihohi da alhakin samun ambaliyar ruwan da ta illata jihohi da dama.

Kungiyoyin sun yi kira da a dinga sanya idanu sosai kan yadda ake sarrafawa da amfani da kudaden da ake bai wa jihohin Nijeriya don yaki da kwararowar hamada.

Binciken da suka gudanar ya gano cewa duk da karbar kudi har Naira biliyan 620 don yaki da kwararowar hamada, jihohin da dama ba su ɗauki wasu matakan rage yiwuwar samun ibtila’in ko rage raddin tasirinsa kan jama’a ba.

An bayyana cewa hakan na dasa ayartambaya kan yadda ake kashe kudaden da ya kamata a inganta muhalli da su a yankunan.

Masu sukar yadda jihohi ke kashe kudaden na cewa ya kamata a dinga sanya idanu sosai tare da bin diddigi a kai a kai kan kudaden na magance kwararowar hamada.

Sun ce hakan zai taimaka wajen magance afkuwar ibtila’in a nan gaba, da kuma tabbatar da cewa jama’a sun amfana da tsarin yadda ya dace don farfaɗowa da sake gina yankunansu.

“Ba mu gani a kasa ba”

A tsakanin 2012 da 2025, jihohin Nijeriya 36 sun karbi jimilillar Naira biliyan 620 don yaƙi da kwararowar hamada.

Ana bai wa jihohi kudaden ne daga asusun gwamnatin tarayya don magance matsalolin muhalli a fadin kasar da suka hada da zaizayar kasa, ambaliyar ruwa, fari da sauran su.

Shugaban Kungiyar Kula da Muhalli ta Nijeriya Afolabi Abiodun ya ce ba sa ganin tasirin kudaden da gwamnatocin ke cewa suna kashewa.

Ya ce “Gwamnati na ikirarin ƙoƙartawa, amma a gaskiyance, ba ma ganin tasirin hakan a kan al’umma. E, akwai kudade da yawa amma ba a ganin suna kawo wani sauyi a tsakanin jama’a.”

Duk shekara a Nijeriya, ana yawan samun ambaliyar ruwan da ke janyo asarar dukiyoyi, a wasu lokutan ma har da rayukan jama’a.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us