NIJERIYA
2 minti karatu
Auta: Sojojin Nijeriya sun kashe ƙasurguman ɗan bindiga a Zamfara
Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda yayin wani samame da ta kai garin Kunchin Kalgo a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a ranar 10 ga watan Yuni.
Auta: Sojojin Nijeriya sun kashe ƙasurguman ɗan bindiga a Zamfara
A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, ta ce rundunar FASAN YAMMA ta kashe ƙasurguman ‘yan ta’adda da suka haɗa da Auta. / Nigerian army
12 Yuni 2025

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda yayin wani samame da ta kai garin Kunchin Kalgo a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a ranar 10 ga watan Yuni.

A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, ta ce rundunar FASAN YAMMA ta kashe ƙasurguman ‘yan ta’adda da suka haɗa da Auta da Abdul Jamilu da kuma Salisu.

“Waɗannan 'yan ta'adda suna da alaƙa da ayyukan tashin hankali da ta'addanci da ake yawan samu a yankin gaba ɗaya. Wannan farmakin dai na nuni da wani gagarumin koma baya ga masu aikata laifuka, wanda ke dagula zaman lafiya da tsaro a yankin,” in ji sanarwar.

Bayanan sirri na farko-farko sun nuna cewa an kashe ƙarin wasu shugabannin ‘yan ta’adda, ciki har da wani da aka fi sani da Babaye a lokacin harin.

Kazalika, a wani lamarin daban, rahotanni sun ce an kashe
Sale Ado Madele da aka fi sani da Sarki, babban ɗan shugaban ‘yan bindiga Ado Alieru.

A wani lamarin mai kama da haka, sojojin sun kuma kashe wasu 'yan ta'adda goma da suka taru a kusa da wata tashar mai da ke garin Danjibga.

Ana kyautata zaton ‘yan ta’addan na cikin wani gungun hadin-gwiwa da Dogo Sule ya haɗa domin kai hari.

Rundunar sojojin Nijeriya ta ce tana ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da kuma maido da dauwamammen zaman lafiya a fadin jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.

Wannan aiki yana ƙara jaddada ƙudurinmu na wargaza hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda tare da gurfanar da masu aikata laifuka a gaban ƙuliya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us