TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta yi watsi da zargin da ake yi na cewa ta ƙi goyon bayan sanarwar Ƙungiyar Hague
Ankara ya yi watsi da zargin da ake yi mata na jinkiri wurin amincewa da matsayar da aka cimmawa a taron Kungiyar Hague, inda Turkiyya ta bayyana cewa tsari tare da jaddada goyon bayanta a ko yaushe ga Falasɗinawa.
Turkiyya ta yi watsi da zargin da ake yi na cewa ta ƙi goyon bayan sanarwar Ƙungiyar Hague
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana zarge-zargen da “marasa tushe” kuma wani ɓangare na yaɗa bayanan ƙarya. / AA
19 Yuli 2025

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi watsi da zarge-zargen da ke cewa ƙasar ta ƙi goyon bayan wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ƙungiyar Hague ta fitar bayan taronta a Colombia a ranakun 15 zuwa 16 ga Yuli, inda take kiran waɗannan zarge-zargen da “marasa tushe” kuma wani ɓangare na yaɗa bayanan ƙarya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, ma’aikatar ta bayyana cewa ana bin tsari kafin shiga cikin sanarwar haɗin gwiwa da ake yi a tarukan ƙasa da ƙasa.

“Kamar yadda duk wanda ke da masaniya da gogewa a irin waɗannan al’amura zai sani, shiga cikin lamura na yanke shawara da sanarwar haɗin gwiwa da ake amincewa da su a tarukan ƙasa da ƙasa yawanci ana bin wani jadawalin da aka tsara,” in ji sanarwar.

A cewar ma’aikatar, ranar ƙarshe da aka tsara don ƙasashe su amince da sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar a taron Bogota ita ce 20 ga Satumba. Zuwa yanzu, ƙasashe 12 kawai daga cikin 30 da suka halarta ne suka bayyana goyon bayansu.

Ci gaba da goyon bayan haƙƙin Falasɗinu

Turkiyya ta jaddada cewa wasu abubuwan da ke cikin sanarwar suna buƙatar haɗin kai tsakanin hukumomi saboda nauyin da ƙasar ke da shi na doka a matakin ƙasa da ƙasa.

“Dukkan hukumomi da ƙungiyoyi masu ruwa da tsaki dole ne su kammala shirye-shiryen da suka dace kafin shiga cikin sanarwar haɗin gwiwa,” in ji ma’aikatar, tana mai jaddada cewa bin tsari ba yana nufin jinkiri na siyasa ba.

Sanarwar ta kuma nuna cewa Turkiyya tana aiwatar da kusan dukkan matakan da aka tsara a cikin sanarwar da aka gabatar.

“Kamar yadda ta saba yi a baya, Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan duk wani yunƙuri da ke kare haƙƙin Falasɗinu,” in ji ma’aikatar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ta gargadi mutane da su guji fassara manufofin Turkiyya game da Gaza ta hanyar abin da ta kira “tunani da aka gina bisa bayanan ƙarya ko mugun nufi.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us