Rundunar Sojin Nijeriya ta kashe masu garkuwa da mutane biyu da kuma kama masu safarar makamai a yankunan Jihohin Filato da Kaduna.
Dakarun Operation Safe Haven ne suka gudanar da wannan aikin a ranar 12 ga Maris ɗin 2025.
“A ranar 12 ga Maris, 2025, sojoji sun gudanar da wani samame a wani bangare na Operation LAFIYAN JAMA'A da ke ci gaba da fatattakar ’yan ta’addan da ke addabar Kuru da Turu a karamar hukumar Jos ta Kudu (LGA) ta Jihar Filato. A yayin farmakin, sojojin sun yi aratabu da masu garkuwa da mutane da ke kusa da babban filin jirgin na Kuru inda suka kashe 2 daga cikin masu laifin da suka mallaki harsashi 18 na 7.62 mm da harsashi 9 na 5.56 x 45 mm,” in ji sanarwar da sojojin suka fitar a ranar Alhamis.
“Bugu da kari, a ranar 12 ga Maris ɗin 2025, sojojin na 3 Division/Operation SAFE HAVEN da ke gudanar da Operation LAFIYAN JAMA'A sun kafa shingayen binciken ababen hawa a hanyar Bokkos zuwa Bot zuwa Mangu a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta jihar Filato.
“Wannan farmakin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri na zirga-zirgar makamai da alburusai a yankin. A yayin farmakin, sojojin sun kama wani dan bindiga mai suna Mista Sengi David mai shekaru 21 da haihuwa wanda ya fito daga kauyen Kopal da ke gundumar Panyam a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato yana rike da ƙundun harsasai na AK-47 guda daya da harsashi 48 na 7.62 mm (na musamman). Waɗanda ake zargin da kuma abubuwan da aka kwato suna hannunsu don gudanar da bincike,” kamar yadda sanarwar ta ƙara bayyanawa.
A wani lamari makamancin haka, sojojin nasu a ranar 11 ga watan Maris ɗin 2025 sun gudanar da wani samame na kamen wani shahararren mai garkuwa da mutane, da ta’addanci kuma ɗan bindiga da aka bayyana sunansa Mista Baraki Paul mai shekaru 22 a unguwar Garaje da ke Karamar Hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.
Wanda ake zargin, ya kasance cikin jerin sunayen jami’an tsaro da ake nema ruwa a jallo bisa laifin yin garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga, tun da farko ya tsere zuwa babban birnin tarayya Abuja domin guje wa kama shi.
Sai dai an kafa masa tarko kan cewa ana son siyan bindigar AK-47 guda daya a kan kudi Naira Miliyan Daya da Dubu Dari Biyar (N1,500,000.00). Wanda ake zargin ya amince kuma ya gana da dakarun da suka nuna masa son saye a wurin da aka zaba a unguwar Garaje inda aka tare shi.
Binciken wanda ake zargin ya kai ga kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, da ƙundun AK-47 daya da kuma harsashi 2 na 7.62 mm (na musamman).